English
A A A A A

Markus 5:21-43
21. Da Yesu ya sāke ƙetarewa cikin jirgin ruwa zuwa ɗaya hayen tafkin, sai taro mai yawa ya taru kewaye da shi yayinda yake a bakin tafkin.
22. Sai ɗaya a cikin masu mulkin majamiʼa, wanda ake kira Yayirus ya zo wurin. Da ganin Yesu, sai ya durƙusa a gabansa,
23. ya roƙe shi da gaske, ya ce, “Ƙaramar diyata tana bakin mutuwa. In ka yarda, ka zo ka ɗibiya hannunka a kanta, domin ta warke, ta kuma rayu.”
24. Sai Yesu ya tafi tare da shi. Babban taron kuma ya bi shi, suna ta matsinsa a kowane gefe.
25. A can kuwa akwai wata mace, wadda ta yi shekaru goma sha biyu tana zub da jini.
26. Ta kuma sha wahala ƙwarai a hannun likitoci da yawa, har ta kashe duk abin da take da shi, amma maimakon samun sauƙi, sai ciwon ya ƙara muni.
27. Da ta ji labarin Yesu, sai ta zo ta bayansa, a cikin taron, ta taɓa rigarsa,
28. domin ta yi tunani cewa, “Ko da rigunarsa ma na taɓa, zan warke.”
29. Nan da take, zub da jininta ya tsaya, sai ta ji a jikinta ta rabu da shan wahalarta.
30. Nan da nan Yesu ya gane cewa, iko ya fita daga gare shi. Sai ya juya a cikin taron ya yi tambaya, “Wa ya taɓa rigata?”
31. Sai almajiransa suka ce, “Kana ganin mutane suna matsinka, duk da haka kana tambaya, ‘Wa ya taɓa ni?’ ”
32. Amma Yesu ya ci gaba da dubawa don yǎ ga wa ya taɓa shi.
33. Matar, da yake ta san abin da ya faru da ita, sai ta zo ta durƙusa a gabansa, da tsoro da rawan jiki, ta kuma gaya masa dukan abin da ya faru.
34. Sai ya ce mata, “Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki tafi cikin salama, kin kuma rabu da dukan wahalarki.”
35. Yayinda Yesu yana cikin magana, sai waɗansu mutane daga gidan Yayirus, mai mulkin majamiʼa, suka zo suka ce, “Diyarka ta rasu. Kada ma ka wahal da Malam.”
36. Yesu bai kula da abin da suka faɗa ba, sai ya ce wa mai mulkin majamiʼar, “Kada ka ji tsoro, ka gaskata kawai.”
37. Bai bar kowa ya bi shi ba, sai Bitrus, Yaƙub da Yohanna ɗanʼuwan Yaƙub.
38. Da suka iso gidan mai mulkin majamiʼar, sai Yesu ya ga ana hayaniya, mutane suna kuka da kururuwa.
39. Sai ya shiga ciki, ya ce musu, “Mene ne dalilin wannan hayaniya da kuka? Yarinyar ba mutuwa ne ta yi ba, barci take yi.”
40. Sai suka yi masa dariya. Bayan ya fitar da su duk waje, sai ya ɗauki mahaifin da mahaifiyar yarinyar tare da almajiran da suke tare da shi, suka shiga inda yarinyar take.
41. Sai ya kama hannunta ya ce mata, “Talita kum!” (Wato, “Ƙaramar yarinya, na ce miki, tashi!”)
42. Nan da nan, sai yarinyar ta tashi ta yi tafiya, (shekarunta goma sha biyu ne). Saboda wannan, suka yi mamaki ƙwarai.
43. Sai ya ba da umarni mai tsanani, kada kowa yǎ san kome game da wannan. Sai ya ce musu, su ba ta wani abu ta ci.