English
A A A A A

Markus 5:1-20
1. Suka ƙetare tafkin suka je yankin Gerasenawa.
2. Da Yesu ya sauka daga jirgin ruwa, sai wani mutum mai mugun ruhu ya fito daga kaburbura, ya tarye shi.
3. Wannan mutumin ya mai da kaburbura gidansa. Kuma ba wanda ya iya ɗaure shi, ko da sarƙa ma.
4. Gama an sha ɗaure shi hannu da ƙafa da sarƙa, amma yakan tsintsinke sarƙar, yǎ kuma karye ƙarafan da suke ƙafafunsa. Ba wanda yake da ƙarfin da zai iya yǎ riƙe shi.
5. Dare da rana, sai yǎ dinga kuka yana ƙuƙƙuje jikinsa da duwatsu a cikin kaburbura da kan tuddai.
6. Da ya hangi Yesu daga nesa, sai ya ruga da gudu, ya zo ya durƙusa a gabansa.
7. Ya yi ihu da babbar murya, ya ce, “Ina ruwanka da ni Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ka rantse da Allah cewa ba za ka ba ni azaba ba!”
8. Domin Yesu ya riga ya faɗa masa, cewa, “Ka fita daga jikin mutumin nan, kai mugun ruhu!”
9. Sai Yesu ya tambaye shi, ya ce, “Mene ne sunanka?” Sai ya amsa, ya ce, “Sunana Legiyon, wato, ‘Tuli,’ domin muna da yawa.”
10. Sai ya yi ta roƙon Yesu, kada yǎ kore su daga wurin.
11. A kan tudun da yake nan kusa kuwa, akwai wani babban garken aladu, suna kiwo.
12. Sai aljanun suka roƙi Yesu, suka ce, “Tura mu cikin aladun nan, ka bari mu shiga cikinsu.”
13. Ya kuwa yarda musu, sai mugayen ruhohin suka fita suka shiga cikin aladun. Garken kuwa, yana da kusan aladu dubu biyu, suka gangara daga kan tudun zuwa cikin tafkin, suka nutse.
14. Masu kiwon aladun kuwa suka ruga da gudu zuwa cikin gari da ƙauyuka, suka ba da wannan labari. Sai mutanen suka fito, domin su ga abin da ya faru.
15. Da suka kai wajen Yesu, sai suka ga mutumin da dā yake da tulin aljanun yana zaune a wurin, sanye da tufafi kuma cikin hankalinsa, sai suka ji tsoro.
16. Waɗanda suka ga abin da ya faru, suka ba da labarin abin da ya faru da mai aljanun, da kuma aladun.
17. Sai mutane suka roƙi Yesu yǎ bar yankinsu.
18. Yesu yana kan shiga cikin jirgin ruwa ke nan, sai mutumin da dā yake da aljanun ya roƙa yǎ bi shi.
19. Yesu bai yardar masa ba, amma ya ce, “Ka tafi gida wurin iyalinka, ka gaya musu babban alherin da Ubangiji ya yi maka, da yadda ya yi maka jinƙai.”
20. Sai mutumin ya tafi, ya yi ta ba da labari a cikin Dekafolis a kan babban alherin da Yesu ya yi masa. Dukan mutane kuwa suka yi mamaki.