A A A A A

Markus 3:20-35
20. Sai Yesu ya shiga wani gida, taro kuma ya sāke haɗuwa, har shi da almajiransa ma ba su sami damar cin abinci ba.
21. Da ʼyanʼuwansa suka sami wannan labari, sai suka tafi don su dawo da shi, suna cewa, “Ai, ya haukace.”
22. Malaman dokokin da suka zo daga Urushalima suka ce, “Ai, yana da Beʼelzebub! Da ikon sarkin aljanu yake fitar da aljanu.”
23. Sai Yesu ya kira su, ya yi musu magana da misalai, ya ce, “Yaya Shaiɗan zai fitar da Shaiɗan?
24. In mulki yana gāba da kansa, wannan mulki ba zai tsaya ba.
25. In gida yana gāba da kansa, wannan gida ba zai tsaya ba.
26. In kuwa Shaiɗan yana gāba da kansa, ya kuma rabu biyu, ba zai tsaya ba, ƙarshensa ya zo ke nan.
27. Hakika, ba mai shiga gidan mai ƙarfi yǎ kwashe dukiyarsa, sai bayan ya ɗaure mai ƙarfin, saʼan nan zai iya yin fashin gidansa.
28. Gaskiya nake gaya muku, za a gafarta duk zunubai da kuma saɓon mutane suka yi.
29. Amma duk wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki, ba za a taɓa gafara masa ba. Ya aikata madawwamin zunubi ke nan.”
30. Ya faɗi haka domin suna cewa, “Yana da mugun ruhu.”
31. Sai mahaifiyar Yesu tare da ʼyanʼuwansa suka iso. Suna tsaye a waje, sai suka aiki wani ciki yǎ kira shi.
32. Taron yana zaune kewaye da shi, sai suka ce masa, “Mahaifiyarka da ʼyanʼuwanka suna waje, suna nemanka.”
33. Ya yi tambaya, ya ce, “Su wane ne mahaifiyata, da ʼyanʼuwana?”
34. Sai ya dubi waɗanda suke zaune kewaye da shi, ya ce, “Ga mahaifiyata da ʼyanʼuwana!
35. Duk wanda yake aikata nufin Allah, shi ne ɗanʼuwana, da ʼyarʼuwata, da kuma mahaifiyata.”