A A A A A

Markus 3:1-19
1. Wani lokaci, da ya sāke shiga majamiʼa, sai ga wani mutum mai shanyayyen hannu.
2. Waɗansu daga cikin mutane suna neman dalilin zargin Yesu, sai suka zuba masa ido, su ga ko zai warkar da shi a ranar Asabbaci.
3. Yesu ya ce wa mutumin mai shanyayyen hannun, “Tashi ka tsaya a gaban kowa.”
4. Sai Yesu ya tambaye su, ya ce, “Me ya kamata a yi bisa ga doka, a ranar Asabbaci: a aikata alheri, ko a aikata mugunta, a ceci rai, ko a yi kisa?” Amma suka yi shiru.
5. Sai ya kalle su da fushi, don taurin zuciyarsu ya ɓata masa rai sosai. Sai ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka,” sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye.
6. Sai Farisiyawa suka fita, suka fara ƙulla shawara da mutanen Hirudus yadda za su kashe Yesu.
7. Yesu da almajiransa suka janye zuwa tafkin, taro mai yawa kuwa daga Galili ya bi shi.
8. Mutane da yawa daga Yahudiya, da Urushalima, da Edom, da kuma yankunan da suke ƙetaren Urdun, da kewayen Taya, da Sidon suka zo wurinsa, don sun ji dukan abubuwan da yake yi.
9. Saboda taron, sai ya ce wa almajiransa su shirya masa ƙaramin jirgin ruwa, don kada mutane su matse shi.
10. Gama ya warkar da mutane da yawa, masu cututtuka suka yi ta ƙoƙarin zuwa gaba, don su taɓa shi.
11. Duk saʼad da mugayen ruhohi suka gan shi, sai fāɗi a gabansa, su ɗaga murya, su ce, “Kai Ɗan Allah ne.”
12. Amma yakan tsauta musu, kada su shaida ko wane ne shi.
13. Yesu ya hau gefen wani dutse, ya kira waɗanda yake so, suka kuma zo wurinsa.
14. Ya naɗa sha biyu-ya kira su manzanni  — don su kasance tare da shi, domin kuma yǎ aike su yin waʼazi,
15. don kuma su sami ikon fitar da aljanu.
16. Ga sha biyun da ya naɗa: Siman (wanda ya ba shi suna Bitrus);
17. Yaƙub ɗan Zebedi da kuma ɗanʼuwansa Yohanna (ga waɗannan kuwa ya sa musu suna Buwarnajis, wato, ʼYaʼyan Tsawa);
18. Andarawus, Filibus, Bartolomeyu, Mattiyu, Toma, Yaƙub ɗan Alfayus, Taddayus, Siman wanda ake kira Zilot,
19. da kuma Yahuda Iskariyot, wanda ya bashe Yesu.