English
A A A A A

Mattiyu 21:23-46
23. Sai Yesu ya shiga filin haikali, yayinda yake koyarwa, sai manyan firistoci da dattawan mutane suka zo wurinsa suka yi tambaya, “Da wane iko kake yin waɗannan abubuwa? Kuma wa ya ba ka wannan iko?”
24. Yesu ya amsa, ya ce, “Ni ma zan yi muku tambaya guda. In kuka ba ni amsa, ni ma zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa.
25. Baftismar Yohanna-daga ina ta fito? Daga sama ce, ko daga mutane?” Sai suka tattauna a junansu suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama,’ zai ce, ‘To, me ya sa ba mu gaskata shi ba?’
26. In kuma muka ce, ‘Daga mutane’ — muna tsoron mutane, gama duk sun ɗauka Yohanna annabi ne.”
27. Saboda haka suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Sai ya ce, “Ni ma ba zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa ba.”
28. “Me kuka gani? An yi wani mutum wanda yake da ʼyaʼya biyu maza. Sai ya je wajen ɗan farin ya ce, ‘Ɗana, yau tafi gonar inabi ka yi aiki.’
29. “Ya amsa ya ce, ‘Ba zan tafi ba,’ amma daga baya ya sāke tunani, ya tafi.
30. “Sai mahaifin ya tafi waje na biyun ya faɗa masa iri magana guda. Sai ya amsa, ya ce, ‘Zan tafi, ranka yǎ daɗe,’ amma bai tafi ba.
31. “Wanne cikin yaran nan biyu ya yi abin da mahaifinsa yake so?” Suka amsa, “Na farin.” Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga mulkin Allah.
32. Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo wurinku don yǎ nuna muku hanyar adalci, ba ku gaskata shi ba, amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata. Har ma bayan kun ga wannan, ba ku tuba kun gaskata shi ba.”
33. “Ku saurari wani misali: An yi wani mai gona wanda ya yi gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa wurin matsin inabi a ciki, ya kuma gina hasumiyar gadi. Saʼan nan ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, ya kuma yi tafiya.
34. Da lokacin girbi ya yi kusa, sai ya aiki bayinsa wajen ʼyan hayan, su karɓo masa ʼyaʼyan inabi.
35. “Amma ʼyan hayan suka kama bayinsa; suka dūke ɗaya, suka kashe ɗaya, suka kuma jajjefi na ukun.
36. Sai ya sāke aiken waɗansu bayi wurinsu, fiye da na dā yawa, amma ʼyan hayan suka yi musu kamar yadda suka yi wa na farin.
37. A ƙarshe, sai ya aiki ɗansa a wurinsu. Ya ce, ‘Za su girmama ɗana.’
38. “Amma da ʼyan hayan suka hangi ɗan, sai suka ce wa juna, ‘Wannan shi ne magājin. Ku zo, mu kashe shi, mu ci gādonsa.’
39. Saboda haka suka kama shi, suka jefar da shi bayan katangar gonar inabin, suka kashe shi.
40. “To, idan mai gonar inabin ya zo, me zai yi da ʼyan hayan nan?”
41. Suka amsa suka ce, “Zai yi wa banzan mutanen nan mugun kisa, yǎ ba da hayar gonar inabin ga waɗansu ʼyan haya, waɗanda za su ba shi rabonsa na amfanin gona a lokacin girbi.”
42. Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karanta a cikin Nassi ba cewa: “ ‘Dutsen da magina suka ƙi shi ne ya zama dutsen kusurwar gini. Ubangiji ne ya aikata wannan, kuma abin mamaki ne a idanunmu’?
43. “Saboda haka, ina gaya muku cewa za a karɓe mulkin Allah daga gare ku, a ba wa mutanen da za su ba da amfani.
44. Duk wanda ya fāɗi a kan dutsen nan, zai kakkarye. Amma duk wanda dutsen nan ya fāɗi a kansa, za a murƙushe shi.”
45. Da manyan firistoci da Farisiyawa suka ji misalan Yesu, sai suka gane cewa da su yake.
46. Suka nemi hanyar kama shi, amma suka ji tsoron taron, don mutane sun ɗauka shi annabi ne.