A A A A A

Markus 1:23-45
23. Nan take, sai wani mutum mai mugun ruhu a majamiʼarsu, ya ɗaga murya ya ce,
24. “Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai-Mai Tsarki nan na Allah!”
25. Yesu ya tsauta masa ya ce, “Yi shiru! Fita daga cikinsa!”
26. Sai mugun ruhun ya jijjiga mutumin da ƙarfi, ya fita daga jikinsa da ihu.
27. Dukan mutane suka yi mamaki, suna tambayar juna suna cewa, “Mene ne haka? Tabɗi! Yau ga sabuwar koyarwa— kuma da iko! Yana ma ba wan mugayen ruhohi umarni, suna kuma yin masa biyayya.”
28. Labari game da shi ya bazu nan da nan koʼina a dukan yankin Galili.
29. Da suka bar majamiʼar, sai suka tafi gidan su Siman da Andarawus, tare da Yaƙub da Yohanna.
30. Surukar Siman tana kwance da zazzaɓi, sai suka gaya wa Yesu game da ita.
31. Sai ya je wajenta, ya kama hannunta, ya ɗaga ta. Zazzaɓin kuwa ya sāke ta, ta kuma yi musu hidima.
32. A wannan yamma, bayan fāɗuwar rana, mutane suka kawo wa Yesu dukan marasa lafiya, da masu aljanu.
33. Duk garin ya taru a ƙofar gidan.
34. Yesu kuwa ya warkar da marasa lafiya da yawa da suke da cututtuka iri-iri. Ya kuma fitar da aljanu da yawa, amma bai yarda aljanun suka yi magana ba, don sun san wane ne shi.
35. Da sassafe, tun da sauran duhu, Yesu ya tashi, ya bar gida, ya tafi wani wurin da ba kowa, a can ya yi adduʼa.
36. Siman da abokansa suka fita nemansa.
37. Da suka same shi, sai suka ce, “Kowa yana nemanka!”
38. Yesu ya amsa, ya ce, “Mu je wani wuri dabam-zuwa ƙauyukan da suke kusa-don in yi waʼazi a can ma. Wannan shi ne dalilin zuwana.”
39. Sai ya tafi koʼina a Galili, yana waʼazi a majamiʼunsu, yana kuma fitar da aljanu.
40. Wani mutum mai kuturta ya zo wurinsa, ya durƙusa ya roƙe shi, ya ce, “In kana so, za ka iya tsabtace ni.”
41. Cike da tausayi, sai Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin, ya ce, “Na yarda, ka tsabtace!”
42. Nan da nan, sai kuturtar ta rabu da shi, ya kuma warke.
43. Yesu ya sallame shi nan take, da gargaɗi mai ƙarfi, cewa,
44. “Ka lura kada ka gaya wa kowa wannan. Amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, ka kuma miƙa hadayun da Musa ya umarta saboda tsarkakewarka, don yǎ zama shaida gare su.”
45. A maimakon haka, sai ya fita, ya fara magana a sake, yana baza labarin. Saboda haka, Yesu bai ƙara iya shiga cikin gari a fili ba, sai dai ya kasance a wuraren da ba kowa. Duk da haka, mutane suka yi ta zuwa wurinsa daga koʼina.