A A A A A

Markus 1:1-22
1. Farkon bishara game da Yesu Kiristi, Ɗan Allah.
2. An rubuta a cikin littafin annabi Ishaya, cewa: “Zan aika ɗan aikina yǎ sha gabanka, wanda zai shirya hanyarka”  —
3. “muryar mai kira a hamada tana cewa, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, ku miƙe hanyoyi dominsa.’ ”
4. Ta haka Yohanna ya zo, yana baftisma a yankin hamada, yana kuma waʼazin baftismar tuba don gafarar zunubai.
5. Dukan ƙauyukan Yahudiya da dukan mutanen Urushalima suka fiffito zuwa wurinsa. Suna furta zunubansu, ya kuwa yi musu baftisma a Kogin Urdun.
6. Yohanna ya sa tufafin gashin raƙumi, yan kuma yi ɗamara da fata. Abincinsa fari ne da kuma zumar jeji.
7. Wannan kuwa shi ne saƙonsa: “A bayana, wanda ya fi ni iko yana zuwa, ban kuwa isa in sunkuya in kunce igiyar takalmansa ba.
8. Ina muku baftisma da ruwa, amma shi zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.”
9. A lokacin, Yesu ya zo daga Nazaret na Galili, Yohanna kuwa ya yi masa baftisma a Urdun.
10. Da Yesu yana fitowa daga ruwan, sai ya ga sama ya buɗe, Ruhu kuma yana saukowa a kansa kamar kurciya.
11. Sai murya ta fito daga sama ta ce, “Kai ne Ɗana, wanda nake ƙauna, da kai kuma nake fari ciki ƙwarai.”
12. Nan da nan, sai Ruhu ya kai shi cikin hamada,
13. ya kuma kasance a hamada kwana arbaʼin, Shaiɗan yana gwada shi. Yana tare da namomin jeji, malaʼiku kuma suka yi masa hidima.
14. Bayan da aka sa Yohanna a kurkuku, sai Yesu ya shigo cikin Galili, yana shelar bisharar Allah.
15. Yana ce, “Lokaci ya yi. Mulkin Allah ya yi kusa. Ku tuba, ku gaskata bishara!”
16. Yayinda Yesu yake tafiya a gaɓar Tekun Galili, sai ya ga Siman da ɗanʼuwansa Andarawus, suna jefa taru cikin tafkin, domin su masunta ne.
17. Yesu ya ce, “Ku zo, ku bi ni, ni kuwa zan mai da ku masuntan mutane.”
18. Nan da nan, suka bar tarunansu, suka bi shi.
19. Da ya yi gaba kaɗan, sai ya ga Yaƙub ɗan Zebedi, da ɗanʼuwansa Yohanna a cikin jirgin ruwa, suna gyaran tarunansu.
20. Ba da ɓata lokaci ba, ya kira su, sai suka bar mahaifinsu Zebedi a cikin jirgin ruwan, tare da ʼyan haya, suka kuwa bi shi.
21. Suka tafi Kafarnahum. Da ranar Asabbaci ta kewayo, sai Yesu ya shiga majamiʼa ya fara koyarwa.
22. Mutane suka yi mamakin koyarwarsa, domin ya koyar da su kamar wanda yake da iko, ba kamar malaman dokoki ba.