English
A A A A A

Mattiyu 27:55-66
55. Akwai mata da yawa a can, suna ƙallo daga nesa. Sun bi Yesu tun daga Galili, suna masa hidima.
56. A cikinsu, akwai Maryamu Magdalin, da Maryamu uwar Yaƙub da Yoses, da kuma uwar ʼyaʼyan Zebedi.
57. Da yamma ta yi, sai ga wani mutum mai arziki daga Arimateya, sunansa Yusuf, wanda shi da kansa almajirin Yesu ne.
58. Ya je wurin Bilatus, ya roƙe shi yǎ ba shi jikin Yesu. Sai Bilatus ya umarta a ba shi.
59. Yusuf ya ɗauki jikin ya nannaɗe shi da zanen lilin mai tsabta.
60. Saʼan nan ya sa shi a sabon kabarinsa, wanda ya haƙa a dutse. Bayan ya gungura wani babban dutse ya rufe bakin kabarin, sai ya tafi abinsa.
61. Maryamu Magdalin da ɗayan Maryamun, suna zaune a wurin, ɗaura da kabarin.
62. Washegari, wato, bayan Ranar Shirye-shirye, sai manya firistoci da Farisiyawa, suka je wurin Bilatus.
63. Suka ce, “Ranka yǎ daɗe, mun tuna, mai ruɗin nan tun yana da rai, ya ce, ‘Bayan kwana uku, zan tashi daga matattu.’
64. Saboda haka, ka ba da umarni, a tsare kabarin sai rana ta uku ɗin. In ba haka ba, almajiransa za su iya zuwa su sace jikin, saʼan nan su faɗa wa mutane cewa, an tashe shi daga matattu. Ruɗin ƙarshen nan fa, sai yǎ fi na farkon muni.”
65. Sai Bilatus ya ce, “Shi ke nan, ku ɗebi soja, ku je ku tsare kabarin iya ƙoƙarinku.”
66. Sai suka je suka tsare kabarin ta wurin buga masa hatimi, suka kuma sa masu gadi.