A A A A A

Mattiyu 27:27-54
27. Sai sojojin gwamna suka ɗauki Yesu suka kai shi Fadar mai mulki, saʼan nan suka tara dukan kamfanin sojoji kewaye da shi.
28. Suka tuɓe shi, suka yafa masa wata jar riga.
29. Suka kuma tuƙa wani rawanin ƙaya, suka sa masa a ka. Suka sa sanda a hannun damansa. Suka durƙusa a gabansa, suka yi masa baʼa, suna cewa, “Ranka yǎ daɗe sarkin Yahudawa!”
30. Suka tattofa masa miyau, suka karɓe sandan, suka yi ta ƙwala masa shi a kai.
31. Bayan sun yi masa baʼa, sai suka tuɓe masa rigar, suka sa masa nasa tufafin. Sai suka tafi da shi, domin su gicciye shi.
32. Suna fitowa ke nan, sai suka sadu da wani mutumin Sairin, mai suna Siman. Sai suka tilasta shi ya ɗauki gicciyen.
33. Sai suka iso wani wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai).
34. A can, suka ba shi ruwan inabi gauraye da wani abu mai ɗaci yǎ sha. Amma da ya ɗanɗana, sai ya ƙi sha.
35. Bayan da suka gicciye shi, sai suka raba tufafinsa a tsakaninsu ta wurin jefa ƙuriʼa.
36. Saʼan nan suka zauna suna tsaronsa.
37. Bisa da kansa kuwa, an kafa rubutun zargin da aka yi masa, da ya ce, “WANNAN SHI NE YESU SARKIN YAHUDAWA.”
38. An gicciye ʼyan fashi biyu tare da shi, ɗaya a damansa, ɗaya kuma a hagunsa.
39. Masu wucewa, suka zazzage shi, suna kaɗa kai,
40. suna cewa, “Kai da za ka rushe haikali, ka kuma gina shi cikin kwana uku, ceci kanka mana! In kai Ɗan Allah ne, ka sauka daga gicciyen!”
41. Haka ma, manyan firistoci da malaman dokoki da kuma dattawa, suka yi ta yin masa baʼa, suna cewa,
42. “Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa! In shi ne Sarkin Israʼila! To, yǎ sauko daga kan gicciyen nan, mu kuwa mu gaskata shi.
43. Ya dogara ga Allah. Bari Allah yǎ cece shi yanzu, in yana sonsa, domin ya ce, ‘Ni Ɗan Allah ne.’ ”
44. Haka ma, ʼyan fashin da aka gicciye tare da shi, suka zazzage shi.
45. Daga saʼa ta shida, har zuwa saʼa ta tara, duhu ya rufe ƙasa duka.
46. Wajen saʼa ta tara, Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani” — wanda yake nufi, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”
47. Saʼad da waɗanda suke tattsaye a wurin suka ji haka, sai suka ce, “Yana kiran Eliya.”
48. Nan da nan, ɗaya daga cikinsu ya ruga, ya sami soso, ya jiƙa shi da ruwan tsami, ya sa a sanda, ya miƙa wa Yesu, yǎ sha.
49. Sauran kuwa suka ce, “Ƙyalle shi mu ga, ko Eliya zai zo yǎ cece shi.”
50. Da Yesu ya sāke ɗaga murya da ƙarfi, sai ya saki ruhunsa.
51. A daidai wannan lokaci, sai labulen haikali ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa. Ƙasa ta jijjiga, duwatsu kuma suka farfashe.
52. Kaburbura suka bubbuɗe, jikunan tsarkaka da yawa kuwa cikin waɗanda da suka mutu, suka tashi.
53. Suka firfito daga kaburbura, saʼan nan bayan tashin Yesu daga matattu, suka shiga birni mai tsarki, suka bayyana ga mutane da yawa.
54. Da jarumin nan tare da waɗanda suke tsaron Yesu, suka ga girgizan ƙasa, da kuma abin da ya faru, sai tsoro ya kama su, suka kuma ce, “Gaskiya, wannan Ɗan Allah ne!”