English
A A A A A

Mattiyu 27:1-26
1. Da wayewar gari, sai dukan manyan firistoci da dattawan mutane suka yanke shawara su kashe Yesu.
2. Suka ɗaure shi, suka tafi da shi, suka ba da shi ga gwamna Bilatus.
3. Saʼad da Yahuda, wanda ya bashe Yesu, ya ga an yanke wa Yesu hukuncin kisa, sai ya yi “da na sani.” Ya je mayar wa manyan firistoci da dattawan kuɗin azurfa talatin ɗin.
4. Ya ce, “Na yi zunubi da na ci amanar marar laifi.” Suka ce masa, “Ina ruwanmu da wannan? Wannan dai ruwanka ne.”
5. Sai Yahuda ya zubar da kuɗin a cikin haikalin ya tafi. Saʼan nan ya je ya rataye kansa.
6. Manyan firistoci suka ɗauki kuɗin, suka ce, “Doka ta hana a sa kuɗin a cikin maʼaji, da yake kuɗin jini ne.”
7. Saboda haka, sai suka yanke shawara su yi amfani da kuɗin suka sayi filin mai yin tukwane, saboda binne baƙi.
8. Shi ya sa ake kiran filin, Filin Jini har yǎ zuwa yau.
9. Sai abin da aka faɗa ta bakin annabi Irmiya ya cika, cewa, “Suka ɗauki azurfa talatin, kuɗin da mutanen Israʼila suka sa a kansa,
10. suka kuma yi amfani da su, suka sayi filin mai yin tukwane, kamar yadda Ubangiji ya umarce ni.”
11. Ana cikin haka, Yesu kuwa yana tsaye a gaban gwamna, sai gwamnan ya tambaye shi, “Kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya ce, “I, haka ne, kamar yadda ka faɗa.”
12. Da manyan firistoci da dattawa suka zarge shi, bai ba da amsa ba.
13. Sai Bilatus ya tambaye shi, ya ce, “Ba ka jin shaidar da suke kawowa a kanka?”
14. Amma Yesu bai ce uffan game da ko ɗaya daga cikin zargin da suka yi masa ba. Har gwamna ya yi mamaki ƙwarai.
15. A wannan irin Biki, gwamna yana da wata alʼada, ta sakin ɗan kurkuku guda wanda taron suka zaɓa.
16. To, a wannan lokaci kuwa suna da wani shahararren ɗan kurkuku da ake kira Barabbas.
17. Saboda haka da taron suka taru, sai Bilatus ya tambaye su, ya ce, “Wane ne a cikinsu kuke so in sakar muku: Barabbas ko Yesu wanda ake kira Kiristi?”
18. Don ya san saboda kishi ne suka ba da Yesu a gare shi.
19. Yayinda Bilatus yake zaune a kan kujerar shariʼa, sai matarsa ta aika masa da wannan saƙo cewa, “Kada ka sa hannunka a kan marar laifin nan, domin na sha wahala ƙwarai, a cikin mafarki yau game da shi.”
20. Amma manyan firistoci da dattawa suka shawo kan taron, su ce, a ba su Barabbas, amma a kashe Yesu.
21. Gwamna ya yi tambaya, ya ce, “Wane ne cikin biyun nan, kuke so in sakar muku?” Suka ce, “Barabbas.”
22. Bilatus ya yi tambaya, “To, me zan yi da Yesu wanda ake kira Kiristi?” Duka suka ce, “A gicciye shi!”
23. Bilatus ya ce, “Don me? Wane laifi ya yi?” Amma suka ƙara ta da ihu, suna cewa, “A gicciye shi!”
24. Da Bilatus ya ga cewa ba ya kaiwa koʼina, sai ma hargitsi ne yake so yǎ tashi, sai ya ɗibi ruwa, ya wanke hannuwansa a gaban taron, ya ce, “Ni kam, ba ruwana da alhakin jinin mutumin nan. Wannan ruwanku ne!”
25. Sai dukan mutane suka amsa, suka ce, “Bari alhakin jininsa yǎ zauna a kanmu da ʼyaʼyanmu!”
26. Sai ya sakar musu Barabbas. Amma ya sa aka yi wa Yesu bulala, saʼan nan ya ba da shi a gicciye.