English
A A A A A

Mattiyu 26:51-75
51. Ganin haka, sai ɗaya daga cikin waɗanda suke tare da Yesu, ya zaro takobinsa ya kai wa bawan babban firist sara, ya fille masa kunne.
52. Sai Yesu ya ce, masa, “Mai da takobinka kube, gama duk masu zare takobi, a takobi za su mutu.
53. Kuna tsammani ba zan iya kira Ubana, nan take kuwa yǎ aiko mini fiye da rundunar malaʼiku goma sha biyu ba?
54. Amma ta yaya za a cika Nassin da ya ce dole haka yǎ faru?”
55. A wannan lokaci sai Yesu ya ce wa taron, “Ina jagorar wani tawaye ne, da kuka fito da takuba da kuma sanduna don ku kama ni? Kowace rana ina zama a filin haikali ina koyarwa, ba ku kuwa kama ni ba.
56. Amma wannan duka ya faru ne don a cika rubuce rubucen annabawa.” Saʼan nan dukan almajiran suka yashe shi suka gudu.
57. Waɗanda suka kama Yesu kuwa suka kai shi wurin Kayifas, babban firist, inda malaman dokoki da dattawa suka taru.
58. Amma Bitrus ya bi daga nesa, har zuwa cikin filin gidan babban firist. Ya shiga, ya zauna tare da masu gadi, don yǎ ga ƙarshen abin.
59. Sai manyan firistoci da ʼyan majalisa duka suka yi ta neman shaidar ƙarya a kan Yesu, don su sami dama su kashe shi.
60. Amma ba su sami ko ɗaya ba, ko da yake masu shaidar ƙarya da yawa sun firfito. A ƙarshe, biyu suka zo gaba,
61. suka furta cewa, “Wannan mutum ya ce, ‘Ina iya rushe haikalin Allah, in sāke gina shi cikin kwana uku.’ ”
62. Saʼan nan babban firist ya miƙe tsaye, ya ce wa Yesu, “Ba ka da wata amsa? Shaidar da mutanen nan suke yi a kanka fa?”
63. Amma Yesu ya yi shiru. Sai babban firist ya ce masa, “Na haɗa ka da Allah mai rai: Faɗa mana in kai ne Kiristi, Ɗan Allah.”
64. Sai Yesu ya amsa, ya ce, “I, haka yake yadda ka faɗa. Sai dai ina gaya muku duka: Nan gaba, za ku ga Ɗan Mutum zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a kan gizagizan sama.”
65. Saʼan nan babban firist ya yage tufafinsa ya ce, “Ya yi saɓo! Don me muke bukatar ƙarin shaidu? Ga shi, yanzu kun dai ji saɓon.
66. Me kuka gani?” Suka amsa, suka ce, “Ya cancanci mutuwa.”
67. Sai suka tottofa masa miyau a fuskarsa, suka kuma bubbuge shi da hannuwansu. Waɗansu kuma suka mammare shi
68. suka ce, “Yi mana annabci, Kiristi. Wa ya buge ka?”
69. To, Bitrus yana nan zaune a filin, sai wata yarinya baiwa, ta zo wurinsa. Ta ce, “Kai ma kana tare da Yesu Bagalile.”
70. Amma ya yi mūsu a gabansu duka. Ya ce, “Ban san abin da kike magana ba.”
71. Saʼan nan ya fito zuwa hanyar shiga, inda wata yarinya kuma ta gan shi, ta ce wa mutanen da suke can, “Wannan mutum ma yana tare da Yesu Banazare.”
72. Ya sāke mūsu har da rantsuwa: yana cewa, “Ban ma san mutumin nan ba!”
73. Bayan ɗan lokaci, sai na tattsaye a wurin, suka hauro wurin Bitrus, suka ce, “Tabbatacce, kai ɗayansu ne, don harshen maganarka, ya tone ka.”
74. Sai ya fara laʼantar kansa, yana ta rantsuwa yana ce musu, “Ban ma san mutumin nan ba!” Nan da take, sai zakara ya yi cara.
75. Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi cewa, “Kafin zakara yǎ yi cara, za ka yi mūsun sani na sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi ta kuka.