English
A A A A A

Mattiyu 26:26-50
26. Yayinda suke cikin cin abinci, Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya ya kuma kakkarya, ya ba wa almajiransa yana cewa, “Ku karɓa ku ci; wannan jikina ne.”
27. Saʼan nan ya ɗauki kwaf, ya yi godiya, ya kuma ba su, yana cewa, “Ku shassha daga cikinsa, dukanku.
28. Wannan jinina ne na sabon alkawari, wanda aka zubar saboda mutane da yawa, don gafarar zunubai.
29. Ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabin nan ba har sai ranar da zan sha shi sabo tare da ku a mulkin Ubana.”
30. Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun.
31. Sai Yesu ya ce musu, “A wannan dare, dukanku za ku ja da baya sabili da ni, gama a rubuce yake cewa: “ ‘Zan bugi makiyayin, tumakin garken kuwa za su fasu.’
32. Amma bayan na tashi, zan sha gabanku zuwa Galili.”
33. Bitrus ya amsa, ya ce, “Ko da duka sun ja da baya sabili da kai, ba zan taɓa ja da baya ba.”
34. Yesu ya amsa, ya ce, “Gaskiya nake gaya maka, a daren nan, kafin zakara yǎ yi cara, za ka yi mūsun sanina sau uku.”
35. Bitrus ya furta, “Ko da ma zan mutu ne tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Dukan sauran almajiran ma suka faɗa haka.
36. Saʼan nan Yesu ya tafi da almajiransa zuwa wani wurin da ake kira Getsemane, ya ce musu, “Ku zauna nan, in je can in yi adduʼa.”
37. Ya ɗauki Bitrus da ʼyaʼya biyun nan na Zebedi tare da shi, sai ya fara baƙin ciki, ya kuma damu.
38. Sai ya ce musu, “Raina yana cike da baƙin ciki har kamar zan mutu. Ku dakata a nan, ku kuma yi tsaro tare da ni.”
39. Da ya yi gaba kaɗan, sai ya fāɗi a ƙasa, ya yi adduʼa, ya ce, “Ubana, in mai yiwuwa ne, a ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba nufina ba, sai naka.”
40. Saʼan nan ya komo wurin almajiransa, ya tarar suna barci. Ya tambayi Bitrus, ya ce, “Ashe, ba za ku iya yin tsaro tare da ni ko na saʼa guda ba?
41. Ku yi tsaro, ku kuma yi adduʼa, don kada ku fāɗi cikin jarraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne.”
42. Ya sāke tafiya sau na biyu, ya yi adduʼa, ya ce, “Ubana, in ba zai yiwu a ɗauke wannan kwaf ba sai na sha shi, to, bari a aikata nufinka.”
43. Da ya dawo, har yanzu ya tarar suna barci, domin idanunsu sun yi nauyi da barci.
44. Saboda haka ya sāke barinsu, ya yi adduʼa sau na uku, yana maimaita iri abu guda.
45. Saʼan nan ya komo wurin almajiransa, ya ce musu, “Har yanzu kuna barci kuna hutawa ba? Ga shi, saʼa ta yi kusa, an kuma bashe Ɗan Mutum a hannuwan masu zunubi.
46. Ku tashi, mu tafi! Ga mai bashe ni nan yana zuwa!”
47. Yayinda yana cikin magana, sai Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, ya iso. Tare da shi kuwa ga taro mai yawa riƙe da takuba da sanduna, manyan firistoci da dattawan mutane ne suka turo su.
48. To, mai bashe shi ɗin, ya riga ya shirya alama da su: “Wanda na yi masa sumba, shi ne mutumin; ku kama shi.”
49. Da zuwansa, sai ya miƙe zuwa wurin Yesu ya ce, “Gaisuwa, Rabbi!” Saʼan nan ya yi masa sumba.
50. Yesu ya amsa, ya ce, “Aboki, yi abin da ya kawo ka.” Saʼan nan mutanen suka matso, suka kama Yesu suka riƙe shi.