A A A A A

Mattiyu 26:1-25
1. Saʼad da Yesu ya gama faɗin dukan waɗannan abubuwa, sai ya ce wa almajiransa,
2. “Kamar yadda kuka sani, Bikin Ƙetarewa sauran kwana biyu-za a kuma ba da Ɗan Mutum don a gicciye shi.”
3. Sai manyan firistoci da dattawan mutane, suka taru a fadan babban firist da ake kira Kayifas,
4. suka ƙulla shawara su kama Yesu da makirci, su kuma kashe shi.
5. Suka ce, “Amma ba a lokacin Biki ba, in ba haka ba mai yiwuwa a yi hargitsi.”
6. Yayinda Yesu yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu,
7. wata mace ta zo wurinsa da wani ɗan tulun alabasta na turaren mai tsada sosai, wanda ta zuba a kansa a lokacin da yake cin abinci.
8. Saʼad da almajiransa suka ga wannan, sai suka yi fushi. Suka ce, “Wannan almubazzaranci fa!
9. Wannan turare ai, da an sayar da shi da kuɗi mai yawa a ba matalauta kuɗin.”
10. Sane da wannan, Yesu ya ce musu, “Me ya sa kuke damun macen nan? Ta yi mini abu mai kyau ne.
11. Matalauta za su kasance tare da ku kullum, amma ni ba zan kasance tare da ku kullum ba.
12. Saʼad da ta zuba turaren nan a jikina, ta shirya ni ne don janaʼizata.
13. Gaskiya nake gaya muku, duk inda aka yi waʼazin bisharan nan a duniya duka, abin da matan nan ta yi, za a riƙa faɗarsa don tunawa da ita.”
14. Sai ɗaya daga cikin Sha Biyun nan-wanda ake kira Yahuda Iskariyot-ya je wurin manyan firistoci
15. ya ce, “Me za ku ba ni, in na bashe shi gare ku?” Sai suka ƙirga masa kuɗi azurfa talatin.
16. Daga wannan lokaci, Yahuda ya yi ta neman zarafin da zai miƙa shi.
17. A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, almajiran suka zo wurin Yesu suka yi tambaya, “Ina kake so mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?”
18. Ya amsa ya ce, “Ku shiga gari wurin wāne, ku ce masa, ‘Malam ya ce, lokacina ya yi kusa. Zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina a gidanka’ ”
19. Saboda haka almajiran suka yi yadda Yesu ya umarce su, suka kuwa shirya Bikin Ƙetarewa.
20. Da yamma ta yi, sai Yesu ya zauna don cin abinci tare da Sha Biyun.
21. Yayinda suke cin abinci, sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”
22. Suka yi baƙin ciki ƙwarai, suka fara ce masa da ɗaya-ɗaya, “Tabbatacce ba ni ba ne, ko, Ubangiji?”
23. Yesu ya amsa, ya ce, “Wanda ya sa hannunsa a kwano tare da ni ne, zai bashe ni.
24. Ɗan Mutum zai tafi kamar yadda aka rubuta game da shi. Amma kaiton mutumin da zai bashe Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da ya fi masa.”
25. Saʼan nan Yahuda, wanda zai bashe shi, ya ce, “Tabbatacce ba ni ba ne, ko, Rabbi?” Yesu ya amsa, ya ce, “I, kai ne.”