A A A A A

Mattiyu 25:31-46
31. “Saʼad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa, tare da dukan malaʼiku, zai zauna a kursiyinsa cikin ɗaukakar sama.
32. Za a tara dukan alʼummai a gabansa, zai kuma raba mutane dabam dabam yadda makiyayi yakan ware tumaki daga awaki.
33. Zai sa tumaki a damansa, awaki kuma a hagunsa.
34. “Saʼan nan Sarki zai ce wa waɗanda suke damansa, ‘Ku zo, ku da Ubana ya yi wa albarka; ku karɓi gādonku, mulkin da aka shirya muku tun halittar duniya.
35. Gama da nake jin yunwa, kun ciyar da ni, da nake jin ƙishirwa, kun ba ni abin sha, da nake baƙunci, kun karɓe ni,
36. da nake bukatar tufafi, kun yi mini sutura, da na yi rashin lafiya, kun lura da ni, da nake kurkuku, kun ziyarce ni.’
37. “Saʼan nan masu adalci za su amsa masa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka da yunwa muka ciyar da kai, ko da ƙishirwa muka ba ka abin sha?
38. Yaushe kuma muka gan ka baƙo muka karɓe ka, ko cikin bukatar tufafi muka yi maka sutura?
39. Yaushe kuma muka gan ka cikin rashin lafiya ko a kurkuku muka ziyarce ka?’
40. “Sarkin zai amsa, ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka yi wa ɗaya daga cikin waɗannan ʼyanʼuwana mafi ƙanƙanta, ni kuka yi wa.’
41. “Saʼan nan zai ce wa waɗanda suke a hagunsa, ‘Ku rabu da ni, laʼanannu, zuwa cikin madawwamiyar wutar da aka shirya don Iblis da malaʼikunsa.
42. Gama da nake jin yunwa, ba ku ba ni abinci ba, da nake jin ƙishirwa, ba ku ba ni abin sha ba,
43. da na yi baƙunci, ba ku karɓe ni ba, da nake bukatar tufafi, ba ku yi mini sutura ba, da na yi rashin lafiya kuma ina a kurkuku, ba ku lura da ni ba.
44. “Su ma za su amsa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka cikin yunwa ko ƙishirwa ko baƙo ko cikin bukatar tufafi ko cikin rashin lafiya ko cikin kurkuku, ba mu taimake ka ba?’
45. “Zai amsa, yǎ ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ba ku yi mini ba ke nan.’
46. “Saʼan nan za su tafi cikin madawwamiyar hukunci, amma masu adalci kuwa za su shiga rai madawwami.”