A A A A A

2 Yohanna 1:1-13
1. Wasiƙa daga Dattijon nan, Zuwa ga uwargida zaɓaɓɓiya da kuma ʼyaʼyanta, waɗanda nake ƙauna da gaske— kuma ba ni kaɗai ba, amma har da dukan waɗanda suka san gaskiya— 
2. saboda gaskiyan nan, wadda take cikinmu za ta kuma kasance tare da mu har abada:
3. Alheri, jinƙai da kuma salama daga Allah Uba da kuma Yesu Kiristi, Ɗan Uba, su kasance tare da mu cikin gaskiya da ƙauna.
4. Na yi farin ciki ƙwarai, da na sami waɗansu ʼyaʼyanki suna tafiya cikin gaskiya, kamar yadda Uba ya umarce mu.
5. Yanzu kuma, uwargida ƙaunatacciya, ba sabon umarni nake rubuta miki ba sai dai wanda muke da shi tun farko. Ina roƙo cewa mu ƙaunaci juna.
6. Ƙauna dai ita ce: mu yi biyayya ga umarnansa. Kamar yadda kuka ji tun da fari, umarninsa shi ne ku yi zaman ƙauna.
7. Masu ruɗi da yawa, waɗanda ba su yarda da zuwan Yesu Kiristi cikin jiki ba, sun riga sun fito duniya. Duk irin mutumin nan mai ruɗi ne kuma magabcin Kiristi.
8. Ku lura don kada ku yi hasarar aikin da kuka yi, sai dai ku sami cikakken lada.
9. Duk wanda ya yi gaba bai kuma ci gaba da bin koyarwar Kiristi ba, ba ya tare da Allah; duk wanda ya ci gaba cikin koyarwan nan kuwa yana da Uban da kuma Ɗan.
10. Duk wanda ya zo wurinku bai kuma kawo koyarwan nan ba, kada ku karɓe shi a gidanku ko ku marabce shi.
11. Duk wanda ya karɓe shi yana tarayya da mugun aikinsa ke nan.
12. Ina da abubuwa da dama da zan rubuta muku, sai dai ba na so in yi amfani da takarda da inki in rubuta. A maimako, ina fata in ziyarce ku in kuma yi magana da ku fuska da fuska, domin farin cikinmu yǎ zama cikakke.
13. ʼYaʼyan ʼyarʼuwarki zaɓaɓɓiya suna gaishe ku.