A A A A A

Ruʼuya ta Yohanna 21:1-27
1. Saʼan nan na ga sabon sama da sabuwar duniya, gama sama na farko da duniya ta farko sun shuɗe, babu kuma wani teku.
2. Na ga Birni Mai Tsarki, sabuwar Urushalima tana saukowa daga sama, daga Allah, a shirye kamar amaryar da aka yi mata ado mai kyau saboda mijinta.
3. Na kuma ji wata babbar murya daga kursiyin tana cewa, “Yanzu mazaunin Allah yana tare da mutane, zai kuma zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kansa kuwa zai kasance tare da su yǎ kuma zama Allahnsu.
4. Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin alʼamura sun shuɗe.”
5. Wannan da yake zaune a kursiyin ya ce. “Ina yin kome sabo!” Sai ya ce, “Rubuta wannan, domin waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma.”
6. Ya ce mini: “An gama. Ni ne Alfa da kuma Omega, na Farko da kuma na Ƙarshe. Duk mai jin ƙishirwa zan ba shi abin sha kyauta daga maɓulɓular ruwan rai.
7. Duk wanda ya ci nasara zai gāji dukan wannan, zan kuma zama Allahnsa, shi kuma zai zama ɗana.
8. Amma matsorata, da marasa bangaskiya, masu ƙazanta, masu kisankai, masu fasikanci, masu sihiri, masu bautar gumaka da dukan maƙaryata-wurinsu zai kasance a cikin tafkin wutan da yake farar wuta mai ci. Wannan fa ita ce mutuwa ta biyu.”
9. Ɗaya daga cikin malaʼikun nan bakwai masu kwanonin nan bakwai cike da annoban nan bakwai na ƙarshe, ya zo ya ce mini “Zo, zan nuna maka amaryar, matar Ɗan Ragon.”
10. Ya kuwa ɗauke ni cikin Ruhu zuwa wani babban dutse mai tsayi, ya kuma nuna mini Birni Mai Tsarki, Urushalima, tana saukowa daga sama, daga Allah.
11. Ya haskaka da ɗaukakar Allah, haskensa kuwa ya yi kamar luʼuluʼu mai daraja sosai, kamar jasfa, yana ƙyalƙyali kamar madubi.
12. Yana da babbar katanga mai tsayi, mai ƙofofi goma sha biyu, da kuma malaʼiku goma sha biyu a ƙofofin. A bisa ƙofofin an rubuta sunayen kabilai goma sha biyu na Israʼila.
13. Akwai ƙofofi uku a gabas, uku a arewa, uku a kudu, uku kuma a yamma.
14. An gina katangar birnin a kan tushen gini goma sha biyu, a kansu kuwa akwai sunayen manzannin sha biyu na Ɗan Ragon.
15. Malaʼikan da ya yi magana da ni yana da sandan awo na zinariya don awon birnin, ƙofofinsa, da kuma katangarsa.
16. Birnin murabbaʼi ne, tsayinsa daidai ne da fāɗinsa. Ya auna birnin da sandarsa ya kuwa sami mil 1, 400 (wajen kilomita 2, 200) tsawonsa, fāɗinsa da kuma tsayinsa daidai suke.
17. Ya auna katangarsa ya kuma sami ƙaurinta kamun 144, bisa ga maʼaunin mutum, wanda malaʼikan ya yi amfani da shi.
18. An yi katangar da jasfa, birnin kuma da zinariya zalla, yana kuma ƙyalli kamar madubi.
19. Tushen ginin katangar birnin kuwa an yi masa adon da kowane irin dutse mai daraja. Tushe na farko an yi shi jasfa, na biyu saffaya, na uku agat, na huɗu zumurrudu,
20. na biyar onis, na shida yakutu, na bakwai kirisolit, na takwas beril, na tara tofaz, na goma kirisofuras, na goma sha ɗaya jasin, na goma sha biyu kuma ametis.
21. Ƙofofi goma sha biyun nan luʼuluʼai goma sha biyu ne, kowace ƙofa an yi ta da luʼuluʼu guda. Babban titin birnin kuwa an yi shi da zinariya zalla, yana kuma ƙyalli kamar madubi.
22. Ban ga haikali a cikin birnin ba, domin Ubangiji Allah Maɗaukaki da kuma Ɗan Ragon ne haikalin birnin.
23. Birnin ba ya bukatar rana ko wata su haskaka shi, gama ɗaukakar Allah tana ba shi haske, Ɗan Ragon kuwa shi ne fitilar birnin.
24. Alʼummai za su yi tafiya cikin hasken birnin, sarakunan duniya kuma za su kawo darajarsu cikin birnin.
25. Ba za a taɓa rufe ƙofofin birnin da rana ba, gama ba za a yi dare a can ba.
26. Za a kawo ɗaukaka da girmar alʼummai a cikin birnin.
27. Babu wani abu marar tsarkin da zai taɓa shiga cikin birnin, babu kuma wani mai aikata abin kunya ko ruɗi da zai shiga, sai dai waɗanda aka rubuta sunayensu a cikin littafin rai na Ɗan Ragon.

Ruʼuya ta Yohanna 22:1-21
1. Sai malaʼikan ya nuna mini kogin ruwan rai, mai ƙyalli kamar madubi, yana gangarawa daga kursiyin Allah da na Ɗan Ragon,
2. yana bin tsakiyar babban titi na birnin. A kowane gefen kogin akwai itacen rai mai ba da ʼyaʼya goma sha biyu, yana ba da ʼyaʼyansa kowane wata. Ganyayen itacen kuwa saboda warkar da alʼummai ne.
3. Ba za a ƙara samun laʼana ba. Kursiyin Allah da na Ɗan Ragon zai kasance a cikin birnin, bayinsa kuma za su yi masa hidima.
4. Za su ga fuskarsa, sunansa kuma zai kasance a goshinsu.
5. Ba za a ƙara yin dare ba. Ba za su bukaci hasken fitila ko hasken rana ba, domin Ubangiji Allah zai haskaka su. Za su kuwa yi mulki har abada abadin.
6. Malaʼikan ya ce mini, “Waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma. Ubangiji, Allahn ruhohin annabawa, ya aiki malaʼikansa, don yǎ nuna wa bayinsa abubuwan da za su faru nan ba da daɗewa ba.”
7. “Ga shi! Ina zuwa da wuri! Mai albarka ne wanda yake kiyaye kalmomin annabcin da suke cikin wannan littafi.”
8. Ni, Yohanna, na ji, na kuma ga abubuwan nan. Kuma saʼad da na ji, na kuma gan su, sai na fāɗi a ƙasa a gaban malaʼikan da yake nuna mini su, don in yi sujada.
9. Amma ya ce mini, “Kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da ʼyanʼuwanka annabawa, da kuma waɗanda suke kiyaye kalmomin wannan littafi. Allah za ka yi wa sujada!”
10. Saʼan nan ya gaya mini cewa, “Kada ka rufe kalmomin annabcin littafin nan, domin lokaci ya yi kusa.
11. Duk mai yin laifi yǎ ci gaba da yin laifi; duk mai aikata ƙazanta yǎ ci gaba da aikata ƙazanta. Duk mai aikata abin da yake daidai, yǎ ci gaba da aikata abin da yake daidai. Kuma duk wanda yake mai tsarki, yǎ ci gaba da yin abin da yake da tsarki.”
12. “Ga shi, ina zuwa da wuri! Ladan da zan bayar yana tare da ni, kuma zan ba wa kowa gwargwadon abin da ya yi.
13. Ni ne Alfa da kuma Omega, na Fari da kuma na Baya, Farko da kuma Ƙarshe.
14. “Masu albarka ne waɗanda suka wanke tufafinsu, don su sami izinin ci daga itacen rai su kuma shiga birnin ta ƙofofi.
15. Waɗanda suke waje kuwa karnuka ne, masu sihiri, masu fasikanci, masu kisankai, masu bautar gumaka, da duk wanda yake ƙaunar ƙarya yake kuma aikata ta.
16. “Ni, Yesu, na aiko malaʼikana ya ba ka wannan shaida saboda ikkilisiyoyi. Ni ne Tushe da kuma Zuriyar Dawuda, da kuma Tauraron Asubahi mai haske.”
17. Ruhu da kuma amarya suna cewa, “Zo!” Duk wanda ya ji kuwa, yǎ ce, “Zo!” Duk mai jin ƙishirwa, yǎ zo; duk mai bukata kuma, yǎ ɗibi ruwan rai kyauta.
18. Ina yin wa duk wanda ya ji kalmomin annabcin wannan littafi gargaɗi: Duk wanda ya ƙara wani abu a kansu, Allah zai ƙara masa annoban da aka bayyana a littafin nan.
19. Duk wanda kuma ya yi ragi a kalmomi daga littafin annabcin nan, Allah zai ɗauke rabonsa na itacen rai da kuma na birnin nan mai tsarki, waɗanda aka bayyana a littafin nan.
20. Shi da ya shaida waɗannan abubuwa, ya ce, “I, ina zuwa da wuri.” Amin. Zo, Ubangiji Yesu!
21. Alherin Ubangiji Yesu yǎ kasance tare da mutanen Allah. Amin.