A A A A A

Ruʼuya ta Yohanna 18:1-24
1. Bayan wannan sai na ga wani malaʼika yana saukowa daga sama. Yana da iko mai girma, aka haskaka duniya da darajarsa.
2. Ya yi kira da babbar murya, ya ce: “Ta fāɗi! Babilon Mai Girma ta fāɗi. Ta zama gidan aljanu da kuma wurin zaman kowace irin mugun ruhu, wurin zaman kowane irin tsuntsu marar tsabta da mai banƙyama.
3. Gama dukan alʼummai sun sha ruwan inabin haukan zinace zinacenta. Sarakunan duniya sun yi zina tare da ita, attajiran duniya kuma sun arzuta da almubazzarancinta.”
4. Sai na ji wata murya daga sama ta ce: “Ku fita daga cikinta, mutanena, don kada zunubanta su shafe ku, don kada wata annobarta ta same ku;
5. gama zunubanta sun yi tsororuwa sun kai sama. Allah kuma ya tuna da laifofinta.
6. Ku sāka mata kamar yadda ta sāka muku; ku sāka mata sau biyu na abin da ta yi. Ku dama mata sau biyu na abin da yake cikin kwaf nata.
7. Ku ba ta isashen azaba da baƙin ciki kamar daraja da kuma jin daɗin da ta ba wa kanta. A zuciyarta takan yi taƙama, ta ce, ‘Ina zama kamar sarauniya; ni ba gwauruwa ba ce, kuma ba zan taɓa yin makoki ba.’
8. Saboda haka a rana ɗaya annobarta za su cim mata: mutuwa, makoki da kuma yunwa. Wuta zai cinye ta, gama Ubangiji Allah mai girma ne, wanda yake shariʼanta ta.
9. “Saʼad da sarakunan duniya da suka yi zina da ita suka kuma yi tarayya cikin jin daɗinta suka ga hayaƙin ƙunarta, za su yi kuka da makoki saboda ita.
10. Don tsoron ganin azabarta za su tsaya daga nesa, su yi kuka suna cewa: “ ‘Kaito! Kaito, Ya birni mai girma. Ya ke Babilon, birni mai iko! Cikin saʼa guda hallakarki ta zo!’
11. “Attajiran duniya za su yi kuka su kuma yi makoki a kanta, domin ba wanda yake ƙara sayen kayayyakinsu— 
12. kayayyakin zinariya, azurfa, duwatsu masu daraja da luʼu-luʼai; lallausan lilin, tufa masu launin shunayya, siliki da jan tufa; da kowane irin katakai masu ƙanshi da kayayyaki na kowane iri da aka yi da hauren giwa, katakai masu tsada, tagulla, baƙin ƙarfe da dutse mai sheƙi;
13. kayayyakin sinnamon da kayan yaji, na turaren wuta, mur da turare, na ruwan inabi da man zaitun, na gari mai laushi da alkama; shanu da tumaki; dawakai da kekunan doki, da jikuna da kuma rayukan mutane.
14. “Za su ce, ‘Amfanin da kike marmari ya kuɓuce. Dukan arzikinki da darajarki sun ɓace, ba kuwa za a ƙara samunsu ba.’
15. Attajiran da suka sayar da waɗannan kayayyaki suka kuma sami arzikinsu daga gare ta za su tsaya daga nesa, cike da tsoron ganin azabarta. Za su yi kuka da makoki
16. su ce: “ ‘Kaito! Kaito, Ya birni mai girma, saye da lallausan lilin, shunayya da kuma ja, mai walƙiya da zinariya, duwatsu masu daraja da kuma luʼuluʼai!
17. Cikin saʼa guda irin wannan dukiya mai yawa ta hallaka!’ ” “Duk matuƙan jirgin ruwa, da dukan waɗanda suke tafiya a jirgin ruwa, maʼaikatanta, da duk masu samun abin zama gari daga teku za su tsaya daga nesa.
18. Saʼad da suka ga hayaƙin ƙunarta, za su yi ihu su ce, ‘An taɓa samun birni kamar wannan babban birnin kuwa?’
19. Za su zuba ƙura a kawunansu, da kuka da makoki za su yi ta kururuwa: “ ‘Kaito! Kaito, Ya birni mai girma, inda dukan waɗanda suke da jiragen ruwa a teku suka arzuta da ɗumbun dukiyarsa! Cikin saʼa ɗaya ta hallaka!
20. Ki yi murna a kanta, Ya sama! Ku yi murna, ku tsarkaka da manzanni da annabawa! Allah ya hukunta shi saboda abin da ya yi muku.’ ”
21. Saʼan nan wani malaʼika mai ƙarfi ya ɗauki dutse kamar girman babban dutsen niƙa ya jefa cikin teku, ya ce: “Da wannan irin giggitawa za a jefar da birnin Babilon mai girma ƙasa, ba za a ƙara ganinta ba.
22. Ba za a ƙara jin ƙarar kiɗin masu garaya da muryar mawaƙa, da na masu bushe-bushe, da na masu busan ƙaho a cikinki ba. Ba za a ƙara samun maʼaikaci na kowace irin sanaʼa a cikinki kuma ba. Ba za a ƙara jin ƙarar dutsen niƙa a cikinki kuma ba.
23. Hasken fitila ba zai ƙara haskakawa a cikinki ba. Ba za a ƙara jin muryar ango da amarya a cikinki ba. Attajiranki, dā su ne manyan mutanen duniya. Ta wurin sihirinki, dukan ƙasashe sun kauce.
24. A cikinta aka sami jinin annabawa, da na tsarkaka, da kuma na dukan waɗanda aka kashe a duniya.”