English
A A A A A

Ruʼuya ta Yohanna 14:1-20
1. Sai na duba, can a gabana kuwa ga Ɗan Rago, tsaye a kan Dutsen Sihiyona, tare da shi akwai kuma mutane 144, 000 waɗanda suke da sunansa da sunan Ubansa a rubuce a goshinsu.
2. Sai na ji ƙara daga sama kamar motsin ruwaye masu gudu, kamar kuma tsawa. Ƙarar da na ji ta yi kamar ta masu garaya da suke kiɗin garayarsu.
3. Suka kuwa rera sabuwar waƙa a gaban kursiyin da kuma a gaban halittu huɗun nan masu rai, da kuma a gaban dattawa. Ba wanda ya iya koyon waƙar sai mutanen nan 144, 000 da aka fansa daga duniya.
4. Waɗannan su ne waɗanda ba su ƙazantar da kansu da mata ba, gama sun kiyaye kansu da tsarki. Suna bin Ɗan Ragon duk inda ya tafi. Su ne aka saya daga cikin mutane aka kuwa miƙa su kamar ʼyaʼyan fari ga Allah da kuma Ɗan Ragon.
5. Ba a sami ƙarya a bakunansu ba; su kuma marasa aibi ne.
6. Sai na ga wani malaʼika yana tashi sama a tsakiyar sararin sama, yana kuma da madawwamiyar bishara wadda zai yi shela ga waɗanda suke zama a duniya-ga kowace alʼumma, kabila, harshe, da kuma jamaʼa.
7. Ya ce da babbar murya, “Ku ji tsoron Allah ku kuma ɗaukaka shi, domin saʼar hukuncinsa ya yi. Ku yi wa wannan da ya halicci sammai, ƙasa, teku, da maɓulɓulan ruwa sujada.”
8. Malaʼika na biyu ya biyo yana cewa, “Ta fāɗi! Babilon Mai Girma ta fāɗi, wadda ta sa dukan alʼummai suka sha ruwan inabin hauka na zinanta.”
9. Malaʼika na uku ya biyo su ya ce da babbar murya, “Duk wanda ya yi wa dabban nan da siffarta sujada ya kuma sami alamarta a goshi ko a hannu,
10. shi ma zai sha ruwan inabin fushin Allah, wanda aka zuba da duk ƙarfinsa a kwaf fushinsa. Za a ba shi azaba da farar wuta mai ci a gaban tsarkakan malaʼiku da na Ɗan Ragon.
11. Hayaƙin azabarsu kuwa zai dinga tashi har abada abadin. Kuma babu hutu dare ko rana wa waɗanda suke wa dabbar da siffarta sujada, ko kuwa ga duk wanda ya sami alamar sunanta.”
12. Wannan yana bukata haƙuri, a gefen tsarkakan da suke biyayya da umarnan Allah suka kuma kasance da aminci ga Yesu.
13. Sai na ji murya daga sama ta ce, “Rubuta: Masu albarka ne matattun da suka mutu cikin Ubangiji daga yanzu zuwa gaba.” “I, za su huta daga faman aikinsu, gama ayyukansu za su bi su” in ji Ruhu.
14. Na duba, can gabana kuwa ga farin girgije, zaune kuma a kan girgijen kuwa ga wani “da ya yi kamar ɗan mutum” tare da rawanin zinariya a kansa da kuma lauje mai kaifi a hannunsa.
15. Sai wani malaʼika ya fito daga haikali ya kuma yi kira da babbar murya ga wannan mai zaune a kan girgijen ya ce, “Ɗauki laujenka ka yi girbi, domin lokacin girbi ya yi, gama amfanin da yake duniya ya nuna.”
16. Sai wannan mai zaune a girgijen ya wurga laujensa a duniya, sai aka kuwa girbe duniya.
17. Wani malaʼika kuma ya fito daga haikali a sama, shi ma yana da lauje mai kaifi.
18. Har yanzu, wani malaʼika mai lura da wuta, ya fito daga bagaden ya yi kira da babbar murya ga wannan wanda yake da lauje mai kaifi, ya ce, “Ɗauki laujenka mai kaifi ka tattara kawunan ʼyaʼyan inabi daga kurangar inabin duniya, domin ʼyaʼyan inabin sun nuna.”
19. Malaʼikan ya wurga laujensa a duniya, ya tattara ʼyaʼyan inabin, ya kuma zuba su cikin babbar wurin matsewar inabin fushin Allah.
20. Aka tattake su a wurin matsi a bayan birni, jini kuwa ya yi ta fitowa daga wurin matsin har tsayinsa ya yi tsawon linzami a bakin doki, nisansa kuma ya kai wajen kilomita 300.