A A A A A

Ruʼuya ta Yohanna 10:1-11
1. Sai na ga wani babban malaʼika yana saukowa daga sama. An lulluɓe shi da girgije, bakan gizo kuma yana kansa; fuskarsa tana kama da rana, ƙafafunsa kuma suna kama da ginshiƙan wuta.
2. Yana riƙe da ɗan ƙaramin naɗaɗɗen littafi, wanda yake a buɗe a hannunsa. Ya kafa ƙafarsa ta dama a kan teku ƙafarsa ta hagu kuma a kan ƙasa,
3. ya kuma yi ihu da ƙarfi kamar rurin zaki. Da ya yi ihun, sai muryoyin tsawan nan bakwai suka yi magana.
4. Saʼad da tsawan nan bakwai kuwa suka yi magana, ina dab da rubutawa; amma na ji wata murya daga sama ta ce, “Rufe abin da tsawan nan bakwai suka faɗa kada ka rubuta.”
5. Sai malaʼikan da na gani na tsaye a teku da ƙasa ya ɗaga hannunsa na dama sama.
6. Ya kuma yi rantsuwa da wannan wanda yake raye har abada abadin, wanda ya halicci sammai da dukan abin da yake cikinsu, duniya da dukan abin da yake cikinta, da kuma teku da dukan abin da yake cikinsa, ya kuma ce, “Babu sauran jinkiri!
7. Amma a ranakun da malaʼika na bakwai na dab da busa ƙahonsa, za a cika asirin Allah, kamar yadda ya sanar wa bayinsa annabawa.”
8. Sai muryar da na ji daga sama ta sāke magana da ni ta ce, “Tafi, ka karɓi naɗaɗɗen littafin da yake a buɗe a hannun malaʼikan da yake tsaye bisa teku da ƙasa.”
9. Sai na je wajen malaʼikan na ce masa yǎ ba ni ƙaramin naɗaɗɗen littafin. Ya ce mini, “Karɓa ka ci. Zai sa cikinka yǎ yi tsami, amma a bakinka zai zama da zaƙi kamar zuma.”
10. Na karɓi ƙaramin naɗaɗɗen littafin daga hannun malaʼikan na kuma ci. Ya yi zaƙi kamar zuma a bakina, amma saʼad da na cinye, cikina ya yi tsami.
11. Saʼan nan aka ce mini, “Dole ne ka sāke yin annabci game da mutane masu yawa, alʼummai, harsuna da kuma sarakuna.”