English
A A A A A

Ruʼuya ta Yohanna 8:1-13
1. Saʼad da ya buɗe hatimi na bakwai, sai aka yi shiru a sama na kusan rabin saʼa.
2. Sai na ga malaʼiku bakwai da suke tsayawa a gaban Allah, a gare su kuwa aka ba da ƙahoni bakwai.
3. Wani malaʼika, da yake da kaskon zinariyar da ake zuba turare, ya zo ya tsaya kusa da bagaden. Aka ba shi turare da yawa don yǎ miƙa tare da adduʼoʼin dukan tsarkaka a bisa bagaden zinariya a gaban kursiyin.
4. Hayaƙin turaren tare da adduʼoʼin tsarkaka, suka hau zuwa gaban Allah daga hannun malaʼikan.
5. Sai malaʼikan ya ɗauki kaskon, ya cika shi da wuta daga bagaden, ya kuma wurga shi bisan duniya; sai aka yi ta yin tsawa, ƙararraki, walƙiya, da kuma girgizar ƙasa.
6. Sai malaʼiku bakwai ɗin nan da suke da ƙahoni bakwai suka shirya don su busa su.
7. Malaʼika na fari ya busa ƙahonsa, sai ga ƙanƙara da wuta haɗe da jini, aka kuma wurga su bisan duniya. Kashi ɗaya bisa uku na duniya ya ƙone, kashi ɗaya bisa uku na itatuwa suka ƙone, dukan ɗanyar ciyawa kuma ta ƙone.
8. Malaʼika na biyu ya busa ƙahonsa, sai ga wani abu kamar babban dutse mai cin wuta, aka jefa cikin teku. Kashi ɗaya bisa uku na teku ya zama jini,
9. kashi ɗaya bisa uku na halittu masu rai da suke cikin tekun suka mutu, kashi ɗaya bisa uku kuma na jiragen ruwa kuma suka hallaka.
10. Malaʼika na uku ya busa ƙahonsa, sai wani babban tauraro mai cin wuta kamar toci, ya fāɗi daga sararin sama, a kan kashi ɗaya bisa uku na koguna da kuma a bisa maɓulɓulan ruwa— 
11. sunan tauraron kuwa Maɗaci. Kashi ɗaya bisa uku na ruwaye ya zama mai ɗaci, mutane da yawa kuma suka mutu saboda shan ruwan, don ɗacinsa.
12. Malaʼika na huɗu ya busa ƙahonsa, sai aka bugi kashi ɗaya bisa uku na rana, kashi ɗaya bisa uku na wata, da kashi ɗaya bisa uku na taurari, har kashi ɗaya bisa uku nasu ya duhunta. Kashi ɗaya bisa uku na yini ya kasance babu haske, haka ma kashi ɗaya bisan uku na dare.
13. Yayinda nake ƙallo, sai na ji gaggafar da take tashi sama a tsakiyar sararin sama ta yi kira da babbar murya ta ce: “Kaito! Kaito! Kaiton mazaunan duniya, in an yi busan sauran ƙahonin da malaʼikun nan uku suke shirin busawa!”