A A A A A

Ruʼuya ta Yohanna 7:1-17
1. Bayan wannan, na ga malaʼiku huɗu, a tsaye a kusurwoyi huɗu na duniya, suna tsare iskoki huɗu na duniya, domin su hana wani iska hurawa a bisan ƙasa ko a bisan teku ko a bisa wani itace.
2. Sai na ga wani malaʼika yana zuwa daga gabas, yana da hatimin Allah mai rai. Ya yi kira da babbar murya wa malaʼikun nan huɗu da aka ba su iko su cuci ƙasa da teku, ya ce:
3. “Kada ku cuci ƙasa ko teku ko kuma itatuwa sai bayan mun sa hatimi a goshin dukan bayin Allahnmu.”
4. Sai na ji yawan waɗanda aka sa musu hatimi: 144, 000 daga dukan kabilan Israʼila.
5. Daga kabilar Yahuda mutum 12, 000 ne aka sa musu hatimin, daga kabilar Ruben mutum 12, 000, daga kabilar Gad mutum 12, 000,
6. daga kabilar Asher mutum 12, 000, daga kabilar Naftali mutum 12, 000, daga kabilar Manasse mutum 12, 000,
7. daga kabilar Simeyon mutum 12, 000, daga kabilar Lawi mutum 12, 000, daga kabilar Issakar mutum 12, 000.
8. Daga kabilar Zebulun mutum 12, 000, daga kabilar Yusuf mutum 12, 000, daga kabilar Benyamin mutum 12, 000.
9. Bayan wannan sai na duba, can a gabana kuwa ga wani taro mai girma, wanda ba mai iya ƙirgawa, daga kowace alʼumma, kabila, mutane da kuma harshe, suna tsaye a gaban kursiyin da kuma gaban Ɗan Ragon nan. Suna saye da fararen tufafi suna kuma riƙe da rassan dabino a hannuwansu.
10. Suka ta da murya da ƙarfi suna cewa: “Ceto na Allahnmu ne, wanda yake zaune a bisan kursiyi, da kuma na Ɗan Ragon.”
11. Dukan malaʼiku suna tsaye kewaye da kursiyin da kuma kewaye da dattawan tare da halittu huɗun nan masu rai. Suka fāɗi da fuskokinsu ƙasa a gaban kursiyin suka kuma yi wa Allah sujada,
12. suna cewa: “Amin! Yabo da ɗaukaka, da hikima da godiya da girma da iko da ƙarfi sun tabbata ga Allahnmu har abada abadin. Amin!”
13. Sai ɗaya daga cikin dattawan ya tambaye ni ya ce, “Waɗannan da suke saye da fararen tufafi-su wane ne, daga ina kuma suka fito?”
14. Na amsa na ce, “Ranka yǎ daɗe, kai ka sani.” Sai ya ce, “Waɗannan su ne waɗanda suka fito daga matsananciyar wahala; sun wanke tufafinsu suka kuma mai da su farare da jinin Ɗan Ragon nan.
15. Saboda haka, “suna a gaban kursiyin Allah suna masa hidima dare da rana a cikin haikalinsa; kuma wannan mai zaune a kursiyin zai shimfiɗa tentinsa a bisansu.
16. Ba za su sāke jin yunwa ba; ba za su kuma sāke jin ƙishirwa ba. Rana ba za ta buga su ba, ko kuma kowane irin zafin ƙuna.
17. Gama Ɗan Ragon da yake a tsakiyar kursiyin zai zama makiyayinsu; zai bi da su zuwa ga maɓulɓular ruwan rai. Allah kuwa zai share dukan hawaye daga idanunsu.”