English
A A A A A

Ruʼuya ta Yohanna 5:1-14
1. Saʼan nan na ga a hannun damar wannan wanda yake zaune a kursiyin naɗaɗɗen littafi da rubutu a ciki da wajensa an kuma hatimce shi da hatimai bakwai.
2. Na kuma ga wani babban malaʼika yana shela da babbar murya cewa, “Wa ya cancanta yǎ ɓalle hatiman nan yǎ kuma buɗe naɗaɗɗen littafin?”
3. Amma ba wani a sama ko a ƙasa ko a ƙarƙashin ƙasan da ya iya buɗe naɗaɗɗen littafin ko ma yǎ duba cikinsa.
4. Na yi ta kuka domin ba a iya samun wanda ya cancanta yǎ buɗe naɗaɗɗen littafin ko yǎ duba cikinsa ba.
5. Sai ɗaya daga cikin dattawan ya ce mini, “Kada ka yi kuka! Duba, Zakin kabilar Yahuda, da kuma Tushen Dawuda ya ci nasara. Ya iya buɗe naɗaɗɗen littafin da hatimansa bakwai.”
6. Saʼan nan na ga Ɗan Rago, yana kamar an yanka, tsaye a tsakiyar kursiyin, halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan an sun kewaye shi. Yana da ƙahoni bakwai da idanu bakwai, waɗanda suke ruhohi bakwai na Allah da aka aika cikin dukan duniya.
7. Ya zo ya karɓi naɗaɗɗen littafin daga hannun dama na wannan wanda yake zaune a kursiyin.
8. Bayan ya karɓa, sai halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan ashirin da huɗu suka fāɗi ƙasa a gaban Ɗan Ragon. Kowanensu yana da garaya kuma suna riƙe da kaskon zinariya cike da turare, waɗanda suke adduʼoʼin tsarkaka.
9. Suka rera sabuwar waƙa: “Ka cancanci ka karɓi naɗaɗɗen littafin ka kuma buɗe hatimansa, domin an kashe ka, da jininka kuma ka sayi mutane wa Allah, daga kowace kabila da harshe da mutane da kuma alʼumma.
10. Ka mai da su masarauta da kuma firistoci, don su yi wa Allahnmu hidima, kuma za su yi mulki a duniya.”
11. Sai na duba na kuma ji muryar malaʼiku masu yawa, yawansu kuwa ya kai dubu dubbai, da kuma dubu goma sau dubu goma. Suka kewaye kursiyin da halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan.
12. Da babbar murya suka rera: “Macancanci ne Ɗan Ragon nan da aka kashe, don yǎ sami iko da wadata da hikima da ƙarfi da girma da ɗaukaka da kuma yabo!”
13. Saʼan nan na ji kowace halitta a sama da ƙasa da ƙarƙashin ƙasa da kuma bisan teku, da kome da yake cikinsu yana rerawa: “Gare shi mai zama a kan kursiyin da kuma ga Ɗan Ragon yabo da girma da ɗaukaka da iko, sun tabbata har abada abadin!”
14. Sai halittu huɗun nan masu rai suka ce, “Amin”, dattawan kuma suka fāɗi suka yi sujada.