A A A A A

2 Bitrus 2:1-22
1. Amma a dā akwai annabawan ƙarya a cikin mutane, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku. A ɓoye za su shigar da karkataccen koyarwa mai hallaka, har ma su yi mūsun Ubangiji mai iko duka wanda ya saye su-suna kawo wa kansu hallaka farat ɗaya.
2. Da yawa za su bi hanyoyinsu na rashin kunya su kuma sa a rena hanyar gaskiya.
3. Cikin kwaɗayinsu waɗannan malaman ƙarya za su cuce ku da tatsuniyoyin da suka ƙaga. Hukuncinsu yana a rataye a kansu tun da daɗewa, hallakarsu kuma ba ta barci.
4. Gama in har Allah bai ƙyale malaʼiku saʼad da suka yi zunubi ba, amma ya tura su cikin lahira, domin a tsare su don hukunci;
5. in har bai ƙyale duniya ta dā ba saʼad da ya kawo ambaliya a kan mutanenta marasa tsoron Allah, amma ya kiyaye Nuhu, mai waʼazin adalci, da kuma waɗansu bakwai;
6. in har ya hukunta biranen Sodom da Gomorra ta wurin ƙone su suka zama toka, ya kuma maishe su misali na abin da zai faru da marasa tsoron Allah;
7. in kuwa har ya ceci Lot, mai adalci, wanda ya damu ainun da ƙazamar rayuwar mutane marasa bin doka;
8. (adon kuwa abin da adalin nan ya yi, ya kuma gani, saʼad da yake a cikinsu, sai kowace rana yakan ji ciwon aikinsu na kangara a zuciyarsa mai adalci) —
9. in haka ne, to, Ubangiji ya san yadda zai ceci mutane masu tsoron Allah daga gwaje-gwaje, yǎ kuma tsare marasa adalci don ranar hukunci, har yǎ zuwa ranar shariʼa.
10. Wannan gaskiya ce musamman ga waɗanda suke bin shaʼawace-shaʼawacen lalaci na mutuntaka, suna kuma rena masu mulki. Da ƙarfin hali da kuma girmankai, waɗannan mutane ba sa tsoro kawo zargin ɓata sunan talikan sama;
11. duk da haka ko malaʼiku ma da suka fi su ƙarfi suka kuma fi su iko, ba sa kawo irin wannan zargi na ɓata suna game da waɗannan talikai a gaban Ubangiji.
12. Amma waɗannan mutane suna yin saɓo a kan abubuwan da ba su fahimta ba. Suna kama da dabbobi marasa hankali, halittun da suke bin abin da jikinsu ya faɗa musu kawai, waɗanda aka haifa don a kama a hallaka, kuma kamar dabbobi su ma za su hallaka.
13. Za a yi musu sakamako da muguntar da suka yi. A raʼayinsu jin daɗi shi ne a yi annashuwa da rana tsaka. Su ƙazamai ne marasa kunya, suna cike da jin daɗin shaʼawace-shaʼawacensu yayinda suke cin biki tare da ku.
14. Idanunsu sun cike da zina, ba sa ƙoshi da yin zunubi; suna jarabtar waɗanda ba tsayayyu ba; gwanaye ne a kan kwaɗayi-laʼanannun iri!
15. Sun bar miƙaƙƙiyar hanya suka bauɗe suna bin hanyar Balaʼam ɗan Beyor, wanda ya yi ƙaunar hakkin mugunta.
16. Amma an tsauta masa saboda laifinsa ta wurin jaki-dabbar da ba ta magana-wadda ta yi magana da muryar mutum ta kuma kwaɓi haukan annabin.
17. Waɗannan mutane maɓulɓulai ne babu ruwa da kuma hazon da guguwar iska take kora. An shirya matsanancin duhu dominsu.
18. Gama suna surutai banza na girmankai, ta wurin son bin fasikanci na mutuntaka, sukan jan hankulan mutanen da suke kuɓucewa daga waɗancan masu zama cikin kuskure.
19. Suna yin musu alkawarin ʼyanci, yayinda su kansu bayi ne ga aikin lalata-gama mutum bawa ne ga duk abin da ya mallake shi.
20. In har sun kuɓuta daga lalacin duniya ta wurin sanin Ubangijimu da kuma Mai Cetonmu Yesu Kiristi sai suka sāke koma a cikin lalacin, har ya rinjaye su, za su fi muni a ƙarshe fiye da farko.
21. Zai fi musu kyau da ba su taɓa sanin hanyar adalci ba, fiye da a ce sun sani saʼan nan su juya bayansu ga umarni mai tsarkin nan da aka ba su.
22. A kansu karin maganan nan gaskiya ce: “Kare ya koma kan amansa,” da kuma, “Alade da aka yi wa wanka, ya koma birgimarsa cikin laka.”