A A A A A

Yaƙub 1:1-27
1. Wasiƙa daga Yaƙub, bawan Allah da kuma na Ubangiji Yesu Kiristi, Zuwa ga kabilan nan goma sha biyu, da suke warwartse a cikin alʼummai: Gaisuwa.
2. Ku ɗauki wannan da farin ciki mai tsabta, ʼyanʼuwana, duk saʼad da gwaje-gwaje na kowane iri suka zo muku,
3. domin kun san cewa gwajin bangaskiyarku yakan haifi ɗaurewa.
4. Dole ɗaurewa ta kammala aikinta don ku zama balagaggu da kuma cikakku, ba ku kuma rasa kome ba.
5. In waninku ya rasa hikima, ya kamata ya roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi.
6. Amma saʼad da ya roƙa, dole yǎ gaskata, ba tare da shakka ba, domin shi mai shakka, yana kama da raƙumar ruwan tekun da iska take kori tana kuma ɓuɓɓugowa.
7. Kada irin wannan mutum yǎ yi tsammani zai sami wani abu daga Ubangiji;
8. shi mai zuciya biyu ne, marar tsai da zuciyarsa wuri ɗaya a cikin duk abin da yake yi.
9. Bari ɗanʼuwan da yake cikin halin ƙasƙanci yǎ yi taƙama a matsayinsa na ɗaukaka.
10. Amma wanda yake mai arziki, ya kamata yǎ yi taƙama a matsayinsa na ƙasƙanci, gama ba zai daɗe ba kamar furen jeji.
11. Gama in rana ta fito ta yi zafi mai tsanani sai ta sa tsiro yǎ yanƙwane tsiro; furensa yǎ kakkaɓe, kyansa kuma yǎ lalace. Haka ma mai arziki zai shuɗe yayinda yake cikin harkarsa.
12. Mai albarka ne mutumin da yake ɗaurewa cikin gwaji, gama bayan ya yi nasara da gwajin, zai sami rawanin rai wanda Allah ya yi alkawari ga waɗanda suke ƙaunarsa.
13. Saʼad da aka jarrabci mutum, kada yǎ ce, “Allah ne yake jarrabtarsa.” Gama ba ya yiwuwa a jarrabci Allah da mugunta, shi kuma ba ya jarrabtar kowa;
14. amma akan jarrabce kowane mutum saʼad da muguwar shaʼawarsa ta janye shi ta kuma rinjaye shi.
15. Saʼan nan, bayan da shaʼawar ta yi ciki, takan haifi zunubi; zunubi kuwa, saʼad da ya balaga yakan haifi mutuwa.
16. Kada a ruɗe ku, ʼyanʼuwana ƙaunatattu.
17. Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.
18. Ya zaɓa yǎ haife mu ta wurin kalmar gaskiya, domin mu zama ʼyaʼyan fari na dukan abin da ya halitta.
19. ʼYanʼuwana ƙaunatattu, ku lura da wannan: Ya kamata kowa yǎ kasance mai saurin saurara, ba mai saurin magana ba, ba kuma mai saurin fushi ba,
20. gama fushin mutum ba ya kawo rayuwar adalcin da Allah yake so.
21. Saboda haka, ku rabu da ƙazamin hali da kuma kowace irin mugunta ku kuma yi naʼam da maganar da aka shuka a cikinku da tawaliʼu, wadda za ta iya cetonku.
22. Kada ku zama masu ji kawai, ku ruɗi kanku. A maimakon haka ku zama masu yin abin da ta ce.
23. Duk wanda yake ji magana ne kawai, bai kuwa aikata abin da ta ce ba, yana kama da mutumin da ya ƙalli fuskarsa a madubi
24. bayan ya ƙalli kansa, saʼad da ya tashi daga wurin, nan da nan sai yǎ manta da kamanninsa.
25. Amma duk mai duba cikakkiyar ƙaʼidan nan ta ʼyanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai yǎ mance ba, sai dai mai yi ne yǎ zartar, to wannan shi za a yi wa albarka a cikin abin da yake yi.
26. In wani ya ɗauki kansa mai addini ne duk da haka bai kame harshensa ba, ruɗin kansa yake yi addininsa kuwa banza ne.
27. Addinin da Allah Ubanmu ya yarda da shi a matsayin mai tsabta da kuma marar aibi shi ne: a kula da marayu da gwauraye cikin damuwoyinsu, a kuma kiyaye kai daga lalacin da duniya take sa wa.