A A A A A

Ibraniyawa 13:1-25
1. Ku ci gaba da ƙaunar juna kamar ʼyanʼuwa.
2. Kada ku manta da yin alheri ga baƙi, gama ta yin haka ne waɗansu suka yi wa malaʼiku hidima, ba da saninsu ba.
3. Ku riƙa tunawa da waɗanda suke a kurkuku kamar tare kuke a kurkuku, da kuma waɗanda ake gwada musu azaba, kamar ku ake yi wa.
4. Aure yǎ zama abin girmamawa ga kowa, a kuma kiyaye gadon aure da tsabta, gama Allah zai hukunta masu zina da kuma dukan masu fasikanci.
5. Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce, “Ba zan taɓa bar ka ba; ba zan taɓa yashe ka ba.”
6. Saboda haka muna iya fitowa gabagaɗi, mu ce, “Ubangiji ne mai taimakona; ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai iya yi mini?”
7. Ku tuna da shugabanninku, waɗanda suka faɗa muku maganar Allah. Ku dubi irin rayuwar da suka yi ku kuma yi koyi da bangaskiyarsu.
8. Yesu Kiristi ba ya sākewa, shi ne a jiya, shi ne a yau, shi ne kuma har abada.
9. Kada a ɗauke muku hankali da sababbin koyarwa dabam dabam. Yana da kyau zukatanmu su ƙarfafa ta wurin alheri, ba ta wurin abinci waɗanda ba su da amfani ga waɗanda suke cinsu.
10. Muna da bagade inda firistocin da suka yi hidima a Wurin kasancewa a duniya ba su da izini su ci.
11. Babban firist yakan ɗauki jinin dabbobi yǎ shiga cikin Wuri Mafi Tsarki a matsayin hadaya ta zunubi, amma jikunan dabbobin akan ƙone su a bayan sansani.
12. Haka ma Yesu ya sha wahala a bayan gari don yǎ tsarkake mutane ta wurin jininsa.
13. Saboda haka, sai mu fita mu je wajensa a bayan sansani, muna ɗaukar kunyar da ya sha.
14. Gama a nan ba mu da dawwamammen birni, sai dai muna zuba ido a kan birnin nan mai zuwa.
15. Saboda haka, ta wurin Yesu, bari mu ci gaba da miƙa hadaya ta yabo ga Allah-yabon leɓuna da yake shaidar sunansa.
16. Kada kuma ku manta yin aikin nagari da kuma taimakon waɗansu, gama da irin waɗannan hadayu ne Allah yake jin daɗi.
17. Ku yi wa shugabanninku biyayya ku kuma miƙa kanku ga ikonsu. Suna lura da ku kuma za su ba da lissafi a gaban Allah. Saboda haka kada ku sa su yi fushi saboda aikinsu, ku sa su yi farin ciki. In ba haka ba za su iya taimakonku ba ko kaɗan.
18. Ku yi mana adduʼa. Mun tabbata cewa muna da lamiri mai kyau, kuma muna da marmari mu yi rayuwa ta bangirma a ta kowace hanya.
19. Ni musamman, ina roƙonku ku yi adduʼa, don a komo da ni a gare ku ba da daɗewa ba.
20. Bari Allah na salama, wanda ta wurin jinin madawwamin alkawari ya ta da Ubangijinmu Yesu daga matattu, wannan Makiyayin tumaki mai girma,
21. yǎ kintsa ku da kowane abu mai kyau domin aikata nufinsa, bari kuma yǎ aikata abin da zai gamshe shi cikinmu, ta wurin Yesu Kiristi, a gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada. Amin.
22. ʼYanʼuwa, ina roƙonku ku yi haƙuri da wannan gargaɗi, don ba wata doguwar wasiƙa ce na rubuta muku ba.
23. Ina so ku san cewa an saki ɗanʼuwanmu Timoti. In ya iso da wuri, zan zo tare da shi in gan ku.
24. Ku gai da dukan shugabanninku da kuma dukan mutanen Allah. Waɗanda suke Italiya suna gaishe ku.
25. Alherin Allah yǎ kasance da ku duka.