English
A A A A A

Ibraniyawa 11:17-40
17. Ta wurin bangaskiya Ibrahim, saʼad da Allah ya gwada shi, sai ya miƙa Ishaku hadaya. Shi da ya karɓi alkawaran ya yi shirin miƙa makaɗaicin ɗansa,
18. ko da yake Allah ya ce masa, “Ta wurin Ishaku ne za a lissafta zuriyarka.”
19. Ibrahim ya yi tunani cewa Allah yana iya ta da matattu, a misalce kuwa, ya sāke karɓan Ishaku daga matattu.
20. Ta wurin bangaskiya ne Ishaku ya albarkaci Yaƙub da Isuwa game da nan gabansu.
21. Ta wurin bangaskiya ne Yaƙub, saʼad da yake bakin mutuwa, ya albarkaci kowane ɗan Yusuf, ya kuma yi sujada yayinda yake jingine a kan sandansa.
22. Ta wurin bangaskiya ne Yusuf, saʼad da kwanakinsa suka yi kusan ƙarewa, ya yi magana game da fitowar Israʼilawa daga Masar ya kuma ba da umarni game da ƙasusuwansa.
23. Ta wurin bangaskiya ne iyayen Musa suka ɓoye shi har wata uku bayan haihuwarsa, domin sun ga cewa shi ba kamar sauran yara ba ne, ba su kuwa ji tsoron umarnin sarki ba.
24. Ta wurin bangaskiya ne Musa, saʼad da ya yi girma, ya ƙi a kira shi ɗan diyar Firʼauna.
25. Ya zaɓa yǎ sha wahala tare da mutanen Allah, maimakon yǎ ji daɗin shaʼawace-shaʼawacen zunubi na ɗan lokaci.
26. Ya ɗauki wulaƙanci domin Kiristi ya fi dukiyar Masar daraja, domin ya zuba ido ga ladansa.
27. Ta wurin bangaskiya ya bar Masar, ba tare da jin tsoron fushin sarki ba; ya kuwa jure domin ya ga wannan wanda ba a iya gani.
28. Ta wurin bangaskiya ya kiyaye Bikin Ƙetarewa ya kuma yayyafa jini, domin kada mai hallakar ʼyaʼyan fari yǎ taɓa ʼyaʼyan fari na Israʼila.
29. Ta wurin bangaskiya ne mutane suka bi ta cikin Jan Teku, sai ka ce a kan busasshiyar ƙasa; amma da Masarawa suka yi ƙoƙari su yi haka, sai aka nutsar da su.
30. Ta wurin bangaskiya ne katangar Yeriko ta rushe, bayan mutane suka yi ta kewaye ta har kwana bakwai.
31. Ta wurin bangaskiya ne ba a kashe Rahab karuwan nan, ta tare da marasa biyayya ba don ta marabci ʼyan leƙan asiri.
32. Me kuma zan faɗa? Ba ni da lokacin da zan ba da labari a kan Gideyon, Barak, Samson, Yefta, Dawuda, Samaʼila, da kuma annabawa,
33. waɗanda ta wurin bangaskiya ne suka ci nasara a kan mulkoki, suka aikata adalci, suka kuma sami abin da aka yi alkawari; waɗanda suka rurrufe bakunan zakoki,
34. suka kashe harshen wuta, suka kuma tsere wa kaifin takobi; waɗanda aka mai da rashin ƙarfinsu ya zama ƙarfi; waɗanda suka yi jaruntaka wajen yaƙi suka kuma fatattaki mayaƙan waɗansu ƙasashe.
35. Mata suka karɓi ƙaunatattunsu da aka sāke tasar daga matattu. Aka azabtar da yawancin mutanen nan, amma suka ƙi a sake su, domin sun tabbata za su sami lada mafi kyau saʼad da aka ta da matattu.
36. Waɗansu suka sha baʼa da bulala. Waɗansu kuwa suka sha ɗauri da sarƙa aka kuma jefa su cikin kurkuku.
37. Aka jajjefe su da duwatsu; aka raba su biyu da zarto; aka kashe su da takobi. Suka yi ta yawo saye da fatun tumaki da na awaki, suka yi zaman rashi, suka sha tsanani da kuma wulaƙanci— 
38. duniya ba ta ma cancanci su zauna a cikinta ba. Suka yi ta yawo a cikin hamada da a kan duwatsu, da cikin kogwanni da kuma cikin ramummuka.
39. Waɗannan duka an yabe su saboda bangaskiyarsu, duk da haka babu waninsu da ya sami abin da aka yi alkawari.
40. Allah ya shirya mana wani abu mafi kyau. Kuma bai so su kai ga makasudin bangaskiyarsu ba sai tare da mu.