English
A A A A A

Ibraniyawa 10:19-39
19. Saboda haka, ʼyanʼuwa, da yake muna da wannan tabbaci na shiga Wuri Mafi Tsarki ta wurin jinin Yesu,
20. ta wurin sabuwa, rayayyiyar hanya kuma wadda aka buɗe mana ta labulen nan, wato, jikinsa,
21. da yake kuma muna da babban firist mai mulkin gidan Allah,
22. bari mu matso kusa da Allah da zuciya mai gaskiya da kuma cikakken tabbaci mai zuwa ta wurin bangaskiya. Bari mu bar zukatan da tsabta, lamirinmu babu mugunta, da kuma jikunanmu a wanke da ruwa.
23. Bari mu tsaya da ƙarfi a kan ga begen da muka ce namu ne, gama shi da ya yi alkawarin, mai aminci ne.
24. Bari kuma mu yi tunani a kan yadda za mu gargaɗe juna ga ƙauna da kuma ayyuka nagari.
25. Kada mu daina taruwa kamar yadda waɗansu suka saba, sai dai mu ƙarfafa juna-tun ba ma da kuka ga Ranan nan tana kusatowa ba.
26. Ba wata hadayar da za a yi don mutanen da suka yanke shawara su yi ci gaba da yin zunubi da gangan bayan sun sami sanin gaskiya.
27. A maimakon haka za su kasance da babban fargabar hukunci da kuma ta ƙunar wuta wadda za ta cinye abokan gāban Allah.
28. Duk wanda ya ƙi ya kiyaye dokar Musa akan kashe shi ba tausayi, a kan shaidar mutum biyu ko uku.
29. Wane irin hukunci mai tsanani ne kuke tsammani zai dace da mutumin da ya nuna rashin bangirma ga Ɗan Allah, wanda ya yi banza da jinin nan na alkawarin da ya tsarkake shi, wanda kuma ya zargi Ruhun alheri?
30. Gama mun san shi, wannan wanda ya ce, “Ramuwa tawa ce; zan rama.” da kuma, “Ubangiji zai yi wa mutanensa hukunci.”
31. Abu mai matuƙar bantsoro ne a fāɗa cikin hannuwan Allah mai rai.
32. Ku tuna da kwanakin nan da suka wuce bayan kun sami haske, saʼad da kuka tsaya daram a tsananin shan wahala.
33. Wani lokaci a fili an tsananta muku aka kuma zage ku aka kuma tsananta muku; a wani lokaci kuma kuka tsaya tare da waɗanda aka yi musu haka.
34. Kuka ji tausayin waɗanda suke cikin kurkuku, da farin ciki kuma kuka yarda ku rabu da dukiyar da aka ƙwace muku, domin ku kanku kun san cewa kuna da madawwamiyar dukiya mafi kyau.
35. Saboda haka kada ku yar da tabbacinku; za a sāka muku a yalwace.
36. Kuna bukata ku jimre don saʼad da kuka aikata nufin Allah, za ku karɓi abin da ya yi alkawari.
37. Gama a cikin ɗan lokaci kaɗan, “Mai zuwan nan zai zo ba kuwa zai yi jinkiri ba.
38. Amma mai adalcina zai rayu ta wurin bangaskiya. In kuwa ya ja da baya, ba zan ji daɗinsa ba.”
39. Amma mu ba na waɗanda suke ja da baya, su kuma hallaka ba ne, amma na waɗanda suka gaskata, suka kuma sami ceto ne.