A A A A A

Ibraniyawa 10:1-18
1. Dokar, inuwa ce kawai ta kyawawan abubuwa masu zuwa-wannan inuwar ba ita ce ainihin abubuwan ba ne. Saboda haka ba za ta taɓa mai da masu matsowa kusa don yin sujada cikakku ta wurin irin hadayun da ake maimaitawa ba fasawa shekara shekara ba.
2. Da a ce za ta iya, da ba su daina miƙa hadayu ba? Ai, da an riga an tsabtace masu yin sujada sau ɗaya tak, da kuma ba za su ƙara damuwa da zunubansu ba.
3. Amma waɗancan hadayu abin tunawa da zunubai ne na kowace shekara,
4. domin ba zai taɓa yiwuwa jinin bijimai da na awaki yǎ kawar da zunubai ba.
5. Saboda haka, saʼad da Kiristi ya shigo duniya, ya ce: “Hadaya da sadaka kam ba ka so, sai dai ka tanadar mini jiki;
6. hadayun ƙonawa da kuma hadayun zunubi ba ka ji daɗin.
7. Sai na ce, ‘Ga ni nan-a rubuce yake cikin naɗaɗɗen littafi na zo in aikata nufinka, Ya Allah.’ ”
8. Da farko ya ce, “Hadayu da sadakoki, hadayun ƙonawa da hadayun zunubi ba ka so, ba ka kuwa jin daɗinsu” (ko da yake doka ta bukaci a yi su).
9. Saʼan nan ya ce, “Ga ni nan, na zo in aikata nufinka.” Ya kawar da na farkon domin yǎ kafa na biyun.
10. Kuma bisa ga wannan nufi, aka mai da mu masu tsarki ta wurin miƙa hadayar jikin Yesu Kiristi sau ɗaya tak.
11. Kowace rana kowane firist yakan tsaya yin hidimar ibadarsa; sau da sau yakan miƙa hadayu iri ɗaya, waɗanda ba za su taɓa kawar da zunubai ba.
12. Amma da Kiristi ya miƙa hadaya ɗaya ta dukan lokaci saboda zunubai, sai ya zauna a hannun dama na Allah.
13. Tun daga lokacin nan yana jira a mai da abokan gābansa matashin ƙafafunsa,
14. gama ta wurin hadayan nan guda ɗaya ya kammala har abada waɗanda ake tsarkake.
15. Ruhu Mai Tsarki ma ya yi mana shaida game da wannan. Da farko ya ce:
16. “Wannan shi ne alkawarin da zan yi da su bayan wannan lokaci, in ji Ubangiji. Zan sa dokokina a cikin zukatansu, in kuma rubuta su a kan zukatansu.”
17. Sai ya ƙara da cewa: “Zunubansu da kurakuransu ba zan ƙara tunawa da su ba. ”
18. In an gafarta zunubai, babu sauran bukatar miƙa hadaya.