A A A A A

Afisawa 5:17-33
17. Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji.
18. Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu.
19. Ku yi zance da juna cikin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya. Ku rera ku kuma yi kiɗe-kiɗe a zuciyarku ga Ubangiji.
20. Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi kuna gode wa Allah Uba a ko mene ne.
21. Ku yi biyayya da juna saboda bangirmar da kuke yi wa Kiristi.
22. Matan aure, ku yi biyayya ga mazanku kamar ga Ubangiji.
23. Gama miji shi ne kan mace yadda Kiristi yake kai da kuma Mai Ceton ikkilisiya, wadda take jikinsa.
24. To, kamar yadda ikkilisiya take biyayya ga Kiristi, haka ma ya kamata mata su yi biyayya ga mazansu cikin kome.
25. Maza, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kiristi ya ƙaunaci ikkilisiya, ya kuma ba da kansa dominta.
26. Ya mai da ikkilisiya mai tsarki ta wurin ikon maganarsa, ya kuma tsabtacce ta ta wurin wanke ta da ruwa.
27. Kiristi ya yi haka don yǎ miƙa wa kansa ikkilisiya mai ɗaukaka da kuma tsarki, marar aibi, marar tabo ko wani lahani.
28. Ta haka, dole maza su ƙaunaci matansu kamar jikunansu. Wanda yake ƙaunar matarsa yana ƙaunar kansa ne.
29. Gama ba wanda ya taɓa ƙin jikinsa, sai dai yǎ ciyar da shi, yǎ kuma kula da shi, kamar yadda Kiristi yake yi wa ikkilisiya— 
30. gama mu gaɓoɓin jikinsa ne.
31. “Saboda haka mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yǎ manne wa matarsa, su biyun su zama jiki ɗaya.”
32. Wannan babban asiri ne, amma na ɗauke shi a matsayin kwatanci ne na Kiristi da ikkilisiya.
33. Duk da haka, dole kowannenku yǎ ƙaunaci matarsa kamar yadda yake ƙaunar kansa, kuma dole matar ta yi biyayya ga mijinta.