A A A A A

Afisawa 5:1-16
1. Ku zama masu koyi da Allah, kamar ƙaunatattun ʼyaʼya
2. ku kuma yi rayuwar ƙauna, kamar yadda Kiristi ya ƙaunace mu ya kuma ba da kansa dominmu a matsayin sadaka mai ƙanshi da kuma hadaya ga Allah.
3. Kada a ma ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata ko kwaɗayi a tsakaninku, domin bai dace da tsarkaka ba.
4. Haka ma bai kamata a sami datti, ƙazamar magana ko zancen banza a cikinku ba, domin ba su dace ba, a maimakon haka sai ku yi ta yin godiya.
5. Ku dai tabbata, ba wani fasiki, ko mai aikin lalata, ko mai kwaɗayin (wanda shi da mai bautar gumaka ɗaya ne), da yake da gādo a mulkin Kiristi da na Allah.
6. Kada wani yǎ ruɗe ku da kalmomin wofi, gama saboda waɗannan abubuwa ne fushin Allah yake zuwa a kan marasa biyayya.
7. Saboda haka kada ku haɗa kai da su.
8. Gama a dā zukatanku sun cika da duhu, amma yanzu ku cika da haske daga Ubangiji. Ku yi rayuwa kamar ʼyaʼyan haske
9. (domin amfanin haske ya kunshi nagarta, adalci da kuma gaskiya)
10. ku nemi abin da zai gamshi Ubangiji.
11. Ku yi nesa da ayyukan duhun da mutane suke yi, a maimakon haka, ku tona su.
12. Gama abin kunya ne a ma faɗi abubuwan da marasa biyayya suke yi a ɓoye.
13. Amma haske zai tona yadda ainihin waɗannan abubuwa suke,
14. gama haske ne yake sa kome yǎ bayyana. Shi ya sa aka ce: “Ka farka, Ya kai mai barci, ka tashi daga matattu, Kiristi kuwa zai haskaka ka.”
15. Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku yi zama irin na marasa hikima, sai dai kamar masu hikima.
16. Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin mugaye ne.