English
A A A A A

2 Tessalonikawa 3:1-18
1. A ƙarshe, ʼyanʼuwa, ku yi mana adduʼa domin saƙon Ubangiji yǎ yi saurin bazuwa a kuma girmama shi, kamar yadda yake a wurinku.
2. Ku kuma yi adduʼa yadda za a cece mu daga mugayen mutane masu mugunta, gama ba kowa ba ne yake da bangaskiya.
3. Ubangiji mai aminci ne, zai ƙarfafa ku, yǎ kuma tsare ku daga mugun nan.
4. Muna da tabbaci cikin Ubangiji cewa kuna bin umarnai da muka yi muku, za ku kuma ci gaba da yin abubuwan da muka umarta.
5. Bari Ubangiji yǎ bi da zukatanku ga ƙaunan nan ta Allah da kuma jimirin nan na Kiristi.
6. A cikin sunan Ubangiji Yesu, muna muku umarni, ʼyanʼuwa, da ku kiyaye kanku daga kowane ɗanʼuwa mai zaman banza da ba ya rayuwa bisa ga koyarwar da kuka karɓa daga wurinmu.
7. Gama ku kanku kun san yadda ya kamata ku bi gurbinmu. Ba mu yi zaman banza saʼad da muke tare da ku ba,
8. ba mu kuwa ci abincin kowa ba tare da ba mu biya ba. A maimakon haka, mun yi aiki dare da rana, muna fama muna wahala kuma don kada mu nawaita wa waninku.
9. Mun yi wannan, ba don ba mu da ʼyancin karɓar irin taimakon nan ba ne, sai dai domin mu zama gurbin da za ku bi.
10. Ko ma a saʼad da muke tare da ku, mun ba ku wannan umarni cewa: “In mutum ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci.”
11. Mun ji cewa waɗansunku suna zaman banza. Ba sa aikin kome; sai shisshigi kurum.
12. Irin waɗannan mutane muna ba da umarni muna kuma gargaɗe su cikin Ubangiji Yesu Kiristi su natsu su kuma nemi abincin da suke ci.
13. Game da ku kuma ʼyanʼuwa, kada ku gaji da yin abin da yake daidai.
14. In wani bai yi biyayya da umarninmu a wannan wasiƙa ba, sai fa ku lura da shi. Kada ku haɗa kai da shi, don yǎ ji kunya.
15. Duk da haka kada ku mai da shi abokin gāba, sai dai ku gargaɗe shi a matsayin ɗanʼuwa.
16. Yanzu, bari Ubangiji mai salama kansa yǎ ba ku salama a kowane lokaci da kuma a ta kowace hanya. Ubangiji yǎ kasance tare da ku duka.
17. Ni, Bulus, nake rubuta wannan gaisuwa da hannuna, wannan ce shaida a kowace wasiƙata, haka nake rubutu.
18. Alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi yǎ kasance tare da ku duka.