A A A A A

Afisawa 4:1-32
1. A matsayina na ɗan kurkuku saboda Ubangiji, ina roƙonku ku yi rayuwar da ta dace da mutanen da Allah ya zaɓa su zama nasa.
2. Kullum ku kasance masu sauƙinkai da kuma hankali; ku zama masu haƙuri, kuna jimrewa da juna cikin ƙauna.
3. Ku yi ƙoƙari sosai ku kiyaye zaman dayan nan da Ruhu ya ba ku, ku yi haka ta wurin zaman tare cikin salama.
4. Dukanku jiki ɗaya ne, kuna kuma da Ruhu guda. An ba ku bege guda saʼad da aka kira ku.
5. Muna da Ubangiji ɗaya, bangaskiya ɗaya, baftisma kuma ɗaya.
6. Allah ɗaya ne wanda yake Uban dukan kome, wanda yake a bisanmu duka, yana aiki ta wurinmu duka, yana kuma a cikinmu duka.
7. Amma ga kowannenmu an ba da alheri bisa ga yadda Kiristi ya rarraba.
8. Shi ya sa aka ce: “Saʼad da ya hau sama, ya bi da kamammu kamar tawagarsa ya kuma ba da baye-baye ga mutane.”
9. (Me “ya hau,” yake nufi, in ba cewa dā ya sauka can ƙarƙashin ƙasa ba?
10. Shi wannan da ya sauka ɗin, shi ne kuma ya hau zuwa can sama, kai, gaba da sammai, don mulkinsa yǎ cika duniya gaba ɗaya.)
11. Shi ne ya ba wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu su zama annabawa, waɗansu su zama masu waʼazi, waɗansu kuma su zama fastoci da malamai.
12. Ya yi haka don yǎ shirya mutanen Allah saboda ayyukan hidima, don a gina jikin Kiristi.
13. Wannan zai ci gaba har sai mun zama ɗaya a cikin bangaskiya da kuma ta wurin fahimtarmu na Ɗan Allah. Saʼan nan za mu zama balagaggu, kamar yadda Kiristi yake, mu kuma zama gaba ɗaya cikakku kamarsa.
14. An yi wannan kuwa don kada mu koma zama kamar yara, muna ta canja zukatanmu game da abin da muka gaskata don kawai wani ya faɗa mana wani abu dabam ko domin wani ya yi wayo ya ruɗe mu, ya sa ƙarya ta zama kamar gaskiya.
15. Ya kamata kullum ƙauna ta sa mu faɗa gaskiya. Ta haka za mu yi girma a kowace hanya mu kuma zama kamar Kiristi, wanda yake kan
16. dukan jiki. Shi ne ya haɗe jiki duka, ya kuma sa dukan gaɓoɓin jiki suna aiki daidai, yayinda kowace gaɓa take aikinta cikin ƙauna.
17. To, ina dai faɗa muku, ina kuma nacewa a kansa cikin Ubangiji, cewa kada ku ci gaba da yin rayuwa kamar yadda Alʼummai suke yi, cikin banzan tunaninsu.
18. Suna a cikin duhu a fahimtarsu, kuma a rabe suke daga ran Allah saboda jahilcin da yake cikinsu ta dalilin taurarewar zukatansu.
19. Ba sa damu da wani abu ko mai kyau ko marar kyau. Rayukansu sun cika da kowace irin ƙazanta da haɗama.
20. Amma ba abin da aka koya muku ke nan ba saʼad da kuka zo ga sanin Kiristi.
21. Da yake kun ji duka game da shi kuma koyi gaskiyar da take cikin Yesu,
22. sai ku tuɓe tsohon mutumin nan naku da kuma rayuwarku ta dā, wanda yake lalacewa saboda shaʼawace-shaʼawacen suke ruɗe ku.
23. A maimakon haka, bar Ruhu yǎ sabunta tunaninku da halayenku.
24. Dole kuma ku sanya sabon hali domin ku sabon mutum ne, wanda aka halitta cikin kamannin Allah, yǎ zama mai adalci, mai tsarki da kuma mai gaskiya.
25. Saboda haka dole kowannenku yǎ bar yin ƙarya yǎ kuma riƙa faɗa wa maƙwabcinsa gaskiya, gama dukanmu gaɓoɓi jiki ɗaya ne.
26. “Cikin fushinku kada ku yi zunubi”: Kada ku bar rana ta fāɗi kuna fushi,
27. kada kuma ku ba wa Iblis dama.
28. Wanda yake sata, yǎ daina sata, dole kuma yǎ yi aiki, yǎ yi wani abu mai amfani da hannuwansa, don yǎ sami abin da zai iya raba da masu bukata.
29. Kada wata ƙazamar magana ta fita daga bakunanku, sai dai abin da yake da amfani don gina waɗansu bisa ga bukatunsu. Ta haka maganarku za ta zama da amfani ga masu jinta.
30. Kada kuma ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, wanda da shi aka hatimce ku da shi don ranar fansa.
31. Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, haushi da fushi, faɗa da ɓata suna, tare da kowace irin ƙeta.
32. Ku yi alheri ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku.