A A A A A

1 Tessalonikawa 2:1-20
1. Kun sani, ʼyanʼuwa, cewa ziyararmu a gare ku ba ta zama a banza ba.
2. Mun riga mun sha wahala, aka kuma zage mu a Filibbi, kamar yadda kuka sani, amma da taimakon Allahnmu muka yi ƙarfin hali muka sanar muku bishararsa duk da matsananciyar gāba.
3. Gama roƙon da muke yi bai fito daga kuskure ko munafunci ba, ba kuwa ƙoƙari muke yi mu yaudare ku ba.
4. A maimako haka, muna magana ne kamar mutanen da Allah ya amince yǎ danƙa musu amanar wannan bishara. Ba ma ƙoƙari mu gamshi mutane sai dai Allah, mai auna zukatanmu.
5. Kun san ba ma taɓa yin daɗin baki ko mu yi ƙoƙarin kasance da halin kwaɗayin da muke ɓoyewa, Allah shi ne shaidarmu.
6. Ba ma neman yabo daga wurin mutane, ko a gare ku, ko ga waɗansu. A matsayinmu na manzannin Kiristi da mun so, da mun nawaita muku,
7. amma muka kasance masu sauƙinkai a cikinku, kamar yadda mahaifiya take lura da ƙananan ʼyaʼyanta.
8. Muka ƙaunace ku ƙwarai har muka ji daɗin bayyana muku, ba bisharar Allah kaɗai ba amma har rayukanmu ma, domin kun zama ƙaunatattu a gare mu.
9. Ba shakka kuna iya tunawa, ʼyanʼuwa, famarmu da kuma wahalarmu; mun yi aiki dare da rana don kada mu zama nauyi wa wani yayinda muke muku waʼazin bisharar Allah.
10. Ku shaidu ne, haka ma Allah, na yadda muka yi zaman tsarki, adalci da kuma marar aibi a cikinku, ku da kuka ba da gaskiya.
11. Gama kun san cewa mun bi da kowannenku yadda mahaifi yakan yi da ʼyaʼyansa,
12. muna ƙarfafa ku, muna taʼazantar da ku, muna kuma gargaɗe ku ku yi rayuwar da za ta cancanci Allah, wanda ya kira ku zuwa mulkinsa da kuma ɗaukakarsa.
13. Muna kuma gode wa Allah ba fasawa domin, saʼad da kuka karɓi maganar Allah, wadda kuka ji daga gare mu, kun karɓe ta ba kamar maganar mutane ba, sai dai kamar yadda take, maganar Allah wadda take aiki a cikinku ku da kuka ba da gaskiya.
14. Gama ku, ʼyanʼuwa, kun zama masu koyi da ikkilisiyoyin Allah a Yahudiya waɗanda suke cikin Kiristi Yesu: Kun sha wahala a hannun mutanen ƙasarku kamar yadda ikkilisiyoyin nan ma suka sha a hannun Yahudawa,
15. waɗanda suka kashe Ubangiji Yesu da annabawa suka kuma kore mu. Ba sa yin aikin da Allah yake so, masu gāba ne kuwa da dukan mutane
16. suna ƙoƙarin hana mu yin magana ga Alʼummai don kada su sami ceto. Ta haka kullum suke ƙara tara tsibin zunubansu. Fushin Allah ya aukar musu a ƙarshe.
17. Amma, ʼyanʼuwa, saʼad da aka raba mu da ku na ɗan lokaci (a jiki, ba a tunani ba), daga cikin marmarinmu mai tsanani mun yi duk abin da muke iya yi mu gan ku.
18. Gama mun so mu zo wurinku-tabbatacce ni, Bulus, na yi ƙoƙari sau da sau-amma Shaiɗan ya hana mu.
19. Gama mene ne begenmu, farin cikinmu, ko kuma rawanin da zai zama mana abin ɗaukaka a gaban Ubangijinmu Yesu saʼad da ya dawo? Ba ku ba ne?
20. Hakika, ku ne ɗaukakarmu da kuma farin cikinmu.