English
A A A A A

Kolossiyawa 2:1-23
1. Ina so ku san irin famar da nake yi saboda ku da kuma waɗanda suke a Lawodiseya, da kuma saboda dukan waɗanda ba su taɓa ganina ido da ido ba.
2. Manufata ita ce a ƙarfafa su su kuma zama ɗaya a cikin ƙauna. Ina so su kasance da cikakken ƙarfin hali domin suna da cikakken fahimtar asirin Allah, wato, Kiristi kansa.
3. Kiristi ne ya sa a san asirin Allah.
4. Ina faɗa muku wannan ne don kada wani yǎ ruɗe ku da daɗin baki.
5. Gama ko da yake ba na nan tare da ku a cikin jiki, ina tunaninku kullum, ina kuma farin ciki da gani kuna rayuwa yadda ya kamata, kuna kuma dāgewarku a kan bangaskiyarku a cikin Kiristi.
6. To, da yake kun karɓi Kiristi Yesu a matsayin Ubangiji, sai ku ci gaba da rayuwa a cikinsa,
7. ku tsaya daram ku kuma ginu a cikinsa, ku sami ƙarfafawa a cikin bangaskiya kamar yadda aka koya muku, kuna kuma cike da godiya.
8. Ku lura kada wani yǎ ruɗe ku da ilimin banza da wofi. Wannan koyarwa ta mutane ce kawai. Ta fito daga ikokin wannan duniya ne ba daga Kiristi ba.
9. Kiristi yana da halin Allah,
10. an kuma maida ku cikakku a cikin Kiristi, wanda yake shi ne kai a kan kowane iko da kuma hukuma.
11. A cikinsa ne kuma aka yi muku kaciya, ba kuwa yin mutum ba, amma wadda Kiristi ya yi muku, ta wurin tuɓe halinku na mutuntaka.
12. Da yake an binne ku tare da shi cikin baftisma haka kuma aka tashe ku tare da shi ta wurin bangaskiyarku a cikin ikon Allah, wanda ya tashe shi daga matattu.
13. Kun zama matattu saboda ku masu zunubi ne kuma saboda halin zunubanku aka ware. Saʼan nan Allah ya sa kuka rayu tare da Kiristi. Ya gafarta mana dukan zunubanmu.
14. Ya soke rubutacciyar doka tare da ƙaʼidodinta, wadda take gāba da mu, take kuma hammaya da mu; ya kuma kawar da ta, ya kafe ta a kan gicciye.
15. Bayan ya ƙwace makaman ikoki da hukumomi, ya kunyata su a sarari, ya ci nasara a bisansu ta wurin gicciye.
16. Saboda haka kada ku bar wani yǎ shariʼanta ku a kan abin da kuke ci ko sha, ko bisa ga abin da ya shafi wani bikin addini, ko bikin Sabon Wata ko na ranar Asabbaci.
17. Waɗannan su ne hoton abubuwan da za su zo; amma Kiristi ne ainihinsu.
18. Kada ku yarda wani yǎ ɓata ku, cewa shi wani abu ne don ya ga wahayi. Irin mutumin nan yakan nuna ƙasƙancin kai na ƙarya, yǎ kuma ce yana yi wa malaʼiku sujada. Irin mutumin nan yana kumbura kansa ba dalili, sai son zuciya irin na halin mutuntaka.
19. Ya yanke dangantaka da Kiristi wanda yake kai, wanda ta gare shi ne dukkan jiki yake a haɗe, yake tsaye ta wurin taimakon gaɓoɓi da jijiyoyi, yana kuma girma kamar yadda Allah yake sa yǎ yi girma.
20. Kun mutu tare da Kiristi. Yanzu ƙaʼidodin wannan duniya ba su da iko a kanku. Don me kuke zama har yanzu kamar ku nasu ne? Kuna biyayya da umarnansu cewa:
21. “Kada ka kama! Kada ka ɗanɗana! Kada ka taɓa”?
22. Irin waɗannan dokoki suna magana a kan abubuwan da ba sa daɗewa. Su ayyukan mutane ne, sun kuma fito daga koyarwar mutane.
23. Yin biyayya da irin waɗannan ƙaʼidodi za su yi kamar su ne abu mafi kyau da za a yi. Sukan yi kamar suna sa a ƙaunaci Allah sosai a kuma kasance da sauƙinkai a kuma kasance da kamunkai. Amma ba su da wani iko a kan shaʼawace shaʼawacenmu.