A A A A A

Afisawa 3:1-21
1. Ni Bulus, ɗan kurkuku na Kiristi Yesu saboda ku Alʼummai.
2. Na tabbata kun ji labarin hidimar alheri na musamman da Allah ya ba ni dominku.
3. Wannan wasiƙa za ta faɗa muku kaɗan game da yadda Allah ya nuna mini shirinsa na asiri.
4. A yayinda kuke karanta wannan, za ku gane abin da na sani game da wannan shirin.
5. Ba a sanar da wannan asiri wa wani a sauran zamanai ba, amma a yanzu an bayyana shi ta wurin Ruhu Mai Tsarki ga manzanninsa da annabawansa.
6. Asirin nan kuwa shi ne cewa ta wurin bishara, Alʼummai sun zama waɗanda za su yi gādo tare da Israʼila, gaɓoɓin jiki ɗaya, abokan tarayya kuma ga alkawaran nan a cikin Kiristi Yesu.
7. Na zama bawan wannan bishara ta wurin baiwar alherin Allah da aka yi mini ta wurin ikonsa da yake aiki a cikina.
8. Ko da yake ni ba kome ba ne a cikin dukan mutanen Allah, ni aka ba wannan baiwa mai daraja don in faɗa wa Alʼummai cewa saboda Kiristi akwai albarkun da suka wuce gaban misali.
9. An zaɓe ni in bayyana wa dukan mutane shirin asirin nan wanda Allah, mahaliccin kome, ya ɓoye shekara da shekaru.
10. Nufinsa shi ne, yanzu, ta wurin ikkilisiya, a sanar wa masu mulki da masu iko a samaniya cewa Allah yana da hikima iri dabam dabam.
11. Wannan shi ne madawwamin shirinsa, kuma an aikata shi ta wurin Kiristi Yesu Ubangijinmu.
12. A cikinsa da kuma ta wurin bangaskiya ne muke da ƙarfin halin zuwa kusa da Allah gabagaɗi.
13. Don haka, ina roƙonku kada ku fid da zuciya saboda abin da ake yi mini a nan. Ai, saboda ku ne nake shan wahalolin nan, saboda haka ya kamata ku ji an girmama an kuma ɗaukaka ku ne.
14. Saboda wannan ne nake a durƙushe a gaban Uba,
15. wanda ya ba wa kowane iyali a sama da ƙasa suna.
16. Ina adduʼa cewa daga yalwar ɗaukakarsa zai ƙarfafa ku da iko daga ciki ta wurin Ruhunsa.
17. Ina adduʼa domin Kiristi yǎ zauna a cikin zukatanku ta wurin bangaskiya. Ina kuma adduʼa saboda ku da kuka kahu sosai cikin ƙauna,
18. ku sami iko, tare da dukan tsarkaka, ku fahimci faɗin, tsawonta da kuma zurfin ƙaunar Kiristi.
19. Ku kuma san wannan ƙauna wadda ta fi gaban sani-domin a cika ku da dukan cikar Allah.
20. Bari ɗaukaka ta tabbata a gare shi wanda yake da ikon yin aiki a cikinmu, yana kuma aikata abubuwa fiye da dukkan abin da muke roƙo ko muke tunani.
21. Bari ɗaukaka ta tabbata a gare shi a cikin ikkilisiya da kuma a cikin Kiristi Yesu, har yǎ zuwa dukan zamanai, har abada abadin! Amin.