A A A A A

Mattiyu 7:1-29
1. “Kada ku shariʼanta wani, in ba haka ba, ku ma, za a shariʼanta ku.
2. Gama da irin shariʼar da kuka yi wa waɗansu, da ita za a shariʼanta ku. Mudun da kuka yi awo da shi, da shi za a yi muku.
3. “Don me kake duban ɗan tsinken da yake idon ɗanʼuwanka, alhali kuwa da gungume a naka ido?
4. Yaya za ka ce wa ɗanʼuwanka, ‘Bari in cire maka ɗan tsinken nan daga idonka,’ alhali kuwa a kowane lokaci akwai gungume a naka ido?
5. Kai munafuki, fara cire gungumen da yake idonka, a saʼan nan za ka iya gani sosai yadda za ka cire ɗan tsinken da yake a idon ɗanʼuwanka.
6. “Kada ku ba karnuka abin da yake mai tsarki; kada kuma ku jefa wa aladu luʼuluʼanku. In kuka yi haka za su tattake su, saʼan nan su juyo su jijji muku ciwo.
7. “Roƙa za a ba ku; nema za ku samu; ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa.
8. Gama duk wanda ya roƙa, akan ba shi; wanda ya nema kuwa, yakan samu, wanda kuma ya ƙwanƙwasa, za a buɗe masa ƙofa.
9. “Wane ne a cikinku in ɗansa ya roƙe shi burodi, sai yǎ ba shi dutse?
10. Ko kuwa in ya roƙe shi kifi, sai yǎ ba shi maciji?
11. In ku da kuke mugaye kun san yadda za ku ba da kyautai masu kyau ga ʼyaʼyanku, balle Ubanku na sama, ba zai fi ku iya ba da abubuwa masu kyau, ga su waɗanda suka roƙe shi ba!
12. Saboda haka, cikin kome ku yi wa waɗansu abin da kuke so su yi muku, gama wannan shi ne duk abin Doka da Annabawa sun kunsa.
13. “Ku shiga ta matsattsiyar ƙofa. Gama ƙofar zuwa hallaka faɗaɗɗiya ce mai sauƙin bi kuma, kuma masu shiga ta cikinta suna da yawa.
14. Amma ƙofar zuwa rai, ƙarama ce matsattsiya kuma, masu samunta kuwa kaɗan ne.
15. “Ku yi hankali da annabawan ƙarya. Sukan zo muku da kamannin tumaki, amma daga ciki mugayen kyarketai ne.
16. Ta wurin aikinsu za ku gane su. Mutane suna iya tsinkan inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya?
17. Haka ma kowane itace mai kyau yakan ba da ʼyaʼya masu kyau, kuma mummunan itace ba ya ba da ʼyaʼya masu kyau.
18. Itace mai kyau ba ya ba da munanan ʼyaʼya, haka kuma mummunan itace ba ya ba da ʼyaʼya masu kyau.
19. Duk itacen da ba ya ba da ʼyaʼya masu kyau sai a sare shi a jefa cikin wuta.
20. Ta haka, ta wurin aikinsu za ku gane su.”
21. “Ba duk mai ce mini, ‘Ubangiji, Ubangiji’, ne zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda yake aikata nufin Ubana da yake sama.
22. Da yawa za su ce mini a wannan rana, ‘Ubangiji, Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci a cikin sunanka ba, ba kuma a cikin sunanka ne muka fitar da aljanu, muka yi abubuwan banmamaki da yawa ba?’
23. Saʼan nan zan ce musu a fili, ‘Ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!’
24. “Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse.
25. Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuma ta hura ta bugi gidan; duk da haka bai fāɗi ba, domin yana da harsashinsa a kan dutse.
26. Amma duk wanda yake jin kalmomin nan nawa bai kuwa aikata su ba, yana kama da wani wawa wanda ya gina gidansa a kan yashi.
27. Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuwa ta hura ta bugi gidan, sai ya fāɗi da mummunar ragargajewa kuwa.”
28. Saʼad da Yesu ya gama faɗin waɗannan abubuwa, sai taron mutanen suka yi mamakin koyarwarsa,
29. domin ya koyar kamar wani wanda yake da iko, ba kamar malamansu na dokoki ba.