English
A A A A A

Mattiyu 6:1-18
1. “Ku yi hankali kada ku nuna ‘ayyukan adalcinku’ a gaban mutane, domin su gani. In kuka yi haka, ba za ku sami lada daga wurin Ubanku da yake cikin sama ba.
2. “Saboda haka saʼad da kake ba wa masu bukata, kada ka yi shelarsa, yadda munafukai suke yi a majamiʼu da kuma kan tituna, don mutane su ba su girma. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun karɓi ladarsu cikakke.
3. Amma saʼad da kake ba wa masu bukata, kada ka yarda hannun hagunka yǎ ma san abin da hannun damarka yake yi,
4. don bayarwarka ta zama a ɓoye. Saʼan nan Ubanka mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka.
5. “Saʼad da kuma kuke adduʼa, kada ku zama kamar munafukai, gama sun cika son yin adduʼa a tsaye a cikin majamiʼu da kuma a bakin titi, don mutane su gan su. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun karɓi ladarsu cikakke.
6. Amma saʼad da kake adduʼa, sai ka shiga ɗakinka, ka rufe ƙofa, ka yi adduʼa ga Ubanka wanda ba a gani. Saʼan nan, Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka.
7. Saʼad da kuma kuke adduʼa, kada ku yi ta maimaita magana, kamar marasa sanin Allah, domin suna tsammani za a ji su saboda yawan maganarsu.
8. Kada ku zama kamarsu, domin Ubanku ya san abin da kuke bukata kafin ma ku roƙe shi.
9. “To fa, ga yadda ya kamata ku yi adduʼa: “ ‘Ubanmu wanda yake cikin sama, a tsarkake sunanka,
10. mulkinka yǎ zo a aikata nufinka a duniya kamar yadda ake yi a sama.
11. Ka ba mu yau abincin yininmu.
12. Ka gafarta mana laifofinmu, kamar yadda mu ma muke gafarta wa masu yin mana laifi.
13. Kada ka kai mu cikin jaraba, amma ka cece mu daga mugun nan. ’
14. Gama in kuna yafe wa mutane saʼad da suka yi muku laifi, Ubanku da yake cikin sama ma zai gafarta muku.
15. Amma in ba kwa yafe wa mutane laifofinsu, Ubanku ma ba zai gafarta muku zunubanku ba.
16. “Saʼad da kuma kuna azumi, kada ku ɓata fuska, yadda munafukai suke yi. Sukan ɓata fuskokinsu domin su nuna wa mutane cewa suna azumi. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun sami ladarsu cikakke.
17. Amma saʼad da kana azumi, ka shafa wa kanka mai, ka wanke fuskarka,
18. domin kada mutane su ga alama cewa kana azumi, sai dai ga Ubanka kaɗai wanda ba a gani; Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka.