A A A A A

Mattiyu 5:27-48
27. “Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’
28. Amma ina gaya muku, duk wanda ya dubi mace, saʼan nan ya yi shaʼawarta a zuci, ya riga ya yi zina ke nan da ita a zuciyarsa.
29. In idonka na dama yana sa ka yin zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta.
30. In kuma hannunka na dama yana sa ka yin zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta.
31. “An kuma faɗa, ‘Duk wanda ya saki matarsa, dole yǎ ba ta takardar saki.’
32. Amma ina gaya muku, duk wanda ya saki matarsa in ba a kan laifin zina ba, ya sa ta zama mazinaciya ke nan, kuma duk wanda ya auri macen da mijinta ya sake, shi ma yana zina ne.
33. “Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutane a dā, ‘Kada ka karya alkawarinka, sai dai ka cika alkawaran da ka yi wa Ubangiji.’
34. Amma ina gaya muku, Kada ku yi rantsuwa sam: ko da sama, domin kursiyin Allah ne;
35. ko da ƙasa, domin matashin ƙafafunsa ne; ko kuma da Urushalima, domin birnin Babban Sarki ne.
36. Kada kuma ka rantse da kanka, domin ba za ka iya mai da ko gashi ɗaya yǎ zama fari ko baƙi ba.
37. Bari ‘I’ naku yǎ zama ‘I’; ‘Aʼa’ naku kuma yǎ zama ‘Aʼa.’ Duk abin da ya wuce haka, to, daga wurin mugun nan ne.
38. “Kun dai ji an faɗa, ‘Ido domin ido, haƙori kuma domin haƙori.’
39. Amma ina gaya muku, Kada ku yi tsayayya da mugun mutum. In wani ya mare ka a kumatun dama, juya masa ɗayan ma.
40. In kuma wani yana so yǎ yi ƙararka yǎ ƙwace rigarka, to, ba shi mayafinka ma.
41. In wani ya tilasta ka yin tafiya mil ɗaya, to, tafi tare da shi mil biyu.
42. Ka ba wa duk wanda ya roƙe ka abu, kada kuma ka hana wa wanda yake neman bashi daga gare ka.
43. “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka, ka kuma ƙi abokin gābanka.’
44. Amma ina gaya muku: Ku ƙaunaci abokan gābanku kuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku adduʼa,
45. don ku zama ʼyaʼyan Ubanku na sama. Shi yakan sa ranarsa ta haskaka a kan mugaye da masu kirki; yakan kuma sako ruwan sama a bisa masu adalci da marasa adalci.
46. In masoyarku kawai kuke ƙauna, wace lada ce gare ku? Ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba?
47. In kuwa kuna gai da ʼyanʼuwanku ne kaɗai, me kuke yi fiye da waɗansu? Marasa bin Allah ma ba haka suke yi ba?
48. Ku fa zama cikakku, yadda Ubanku na sama yake cikakke.