A A A A A

Mattiyu 5:1-26
1. Ganin taron mutane, sai ya hau kan gefen dutse ya zauna. Almajiransa kuwa suka zo wurinsa,
2. sai ya fara koya musu yana cewa:
3. “Masu albarka ne waɗanda suke matalauta a ruhu, gama mulkin sama nasu ne.
4. Masu albarka ne waɗanda suke makoki, gama za a yi musu taʼaziyya.
5. Masu albarka ne waɗanda suke masu tawaliʼu, gama za su gāji duniya.
6. Masu albarka ne waɗanda suke jin yunwa da ƙishirwa saboda adalci, gama za a ƙosar da su.
7. Masu albarka ne waɗanda suke masu jinƙai, gama za a nuna musu jinƙai.
8. Masu albarka ne waɗanda suke masu tsabtar zuciya, gama za su ga Allah.
9. Masu albarka ne waɗanda suke masu ƙulla zumunci, gama za a kira su ʼyaʼyan Allah.
10. Masu albarka ne waɗanda ake tsananta musu saboda adalci, gama mulkin sama nasu ne.
11. “Masu albarka ne ku saʼad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku, saboda ni.
12. Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa yana a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.
13. “Ku ne gishirin duniya, amma in gishiri ya rabu da daɗin ɗanɗanonsa, yaya za a sāke mai da daɗin ɗanɗanonsa? Ba shi da sauran amfani, sai dai a zubar da shi mutane kuma su tattaka.
14. “Ku ne hasken duniya. Birnin da yake a bisan tudu ba ya ɓoyuwa.
15. Mutane ba sa ƙuna fitila su rufe ta da murfi. A maimako, sukan ajiye ta a kan alkuki, takan kuma ba da haske ga kowa a cikin gida.
16. Haka ma, bari haskenku yǎ haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu kyau, su kuwa yabi Ubanku da yake cikin sama.
17. “Kada ku yi tsammani na zo ne domin in kawar da Doka ko kuma Annabawa; ban zo domin in kawar da su ba ne, sai dai domin in ciccika su.
18. Gaskiya nake gaya muku, sai sama da ƙasa sun shuɗe, babu ko ɗan wasali, babu wani ɗigo ta kowace hanya da zai ɓace daga Dokar, sai an cika kome.
19. Duk wanda ya karya ɗaya daga cikin mafi ƙanƙanta na umarnan nan, ya kuma koya wa waɗansu su yi haka, za a ce da shi mafi ƙanƙanta a mulkin sama. Amma duk wanda ya aikata, ya kuma koyar da waɗannan umarnai, za a kira shi mai girma a cikin mulkin sama.
20. Gama ina faɗa muku cewa in dai adalcinku bai fi na Farisiyawa da na malaman dokoki ba, faufau, ba za ku shiga mulkin sama ba.
21. “Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā cewa, ‘Kada ka yi kisankai; kuma duk wanda ya yi kisankai za a hukunta shi.’
22. Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da ɗanʼuwansa, za a hukunta shi. Kuma duk wanda ya ce wa ɗanʼuwansa ‘Raka,  ’ za a kai shi gaban Majalisa. Amma duk wanda ya ce, ‘Kai wawa!’ Zai kasance a hatsarin shiga jahannama ta wuta.
23. “Saboda haka, in kana cikin ba da baikonka a kan bagade, a can kuwa ka tuna cewa ɗanʼuwanka yana riƙe da kai a zuci,
24. sai ka bar baikonka a can gaban bagade. Ka je ka shirya tukuna da ɗanʼuwanka; saʼan nan ka zo ka ba da baikonka.
25. “Ka yi hanzari ka shirya alʼamura da maƙiyinka wanda yake ƙararka a kotu. Ka yi haka, tun kana tare da shi a kan hanya, in ba haka ba, zai miƙa ka ga alƙali, alƙali kuma yǎ miƙa ka ga ɗan sanda, mai yiwuwa kuwa a jefa ka a kurkuku.
26. Gaskiya nake gaya maka, ba za ka fita ba, sai ka biya kobo na ƙarshe.