English
A A A A A

Mattiyu 4:1-25
1. Saʼan nan Ruhu ya kai Yesu cikin hamada domin Iblis yǎ gwada shi.
2. Bayan ya yi azumi yini arbaʼin da kuma dare arbaʼin, sai ya ji yunwa.
3. Sai mai gwajin ya zo wurinsa ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka ce wa duwatsun nan su zama burodi.”
4. Yesu ya amsa, ya ce, “A rubuce yake: ‘Ba da burodi kaɗai mutum yake rayuwa ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga bakin Allah.’ ”
5. Saʼan nan Iblis ya kai shi birni mai tsarki, ya sa shi ya tsaya a kan wuri mafi tsayi duka na haikali.
6. Ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, dira ƙasa. Gama a rubuce yake: “ ‘Zai umarci malaʼikunsa game da kai, za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’ ”
7. Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake kuma cewa: ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ”
8. Har wa yau, Iblis ya kai shi bisa wani dutse mai tsawo, ya nunnuna masa dukan mulkokin duniya da darajarsu.
9. Ya ce, “Zan ba ka dukan wannan, in ka durƙusa ka yi mini sujada.”
10. Sai Yesu ya ce masa, “Rabu da ni, Shaiɗan! Gama a rubuce yake: ‘Yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai kuma za ka bauta wa.’ ”
11. Saʼan nan Iblis ya bar shi, malaʼiku kuwa suka zo suka yi masa hidima.
12. Da Yesu ya ji labari cewa an sa Yohanna a kurkuku, sai ya koma zuwa Galili.
13. Barin Nazaret, sai ya je ya zauna a Kafarnahum, wadda take a bakin tafki wajen Zebulun da Naftali— 
14. don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa:
15. “Ƙasar Zebulun da ƙasar Naftali, hanyar zuwa teku, a bakin Urdun, Galili ta Alʼummai— 
16. mutanen da suke zama cikin duhu sun ga babban haske; a kan waɗanda suke zama a ƙasar inuwar mutuwa kuwa haske ta haskaka.”
17. Tun daga wannan lokaci, Yesu ya fara waʼazi yana cewa, “Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.”
18. Da Yesu yana kan tafiya a bakin Tekun Galili, sai ya ga waɗansu ʼyanʼuwa guda biyu, Siman wanda ake kira Bitrus da ɗanʼuwansa Andarawus. Suna jefa taru a tafki, gama su masunta ne.
19. Sai Yesu ya ce, “Zo, ku bi ni, ni kuwa zan mai da ku masuntan mutane.”
20. Nan da nan suka bar tarunsu suka bi shi.
21. Da ya ci gaba daga nan, sai ya ga waɗansu ʼyanʼuwa guda biyu, Yaƙub ɗan Zebedi da ɗanʼuwansa Yohanna. Suna cikin jirgin ruwa tare da mahaifinsu Zebedi, suna shirya tarunsu. Yesu ya kira su,
22. nan take suka bar jirgin ruwan da mahaifinsu suka kuwa bi Yesu.
23. Yesu ya zazzaga dukan Galili, yana koyarwa a cikin majamiʼunsu, yana waʼazin labari mai daɗi na mulkin sama, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiyar mutane.
24. Labarinsa ya bazu koʼina a Suriya, mutane kuwa suka kawo masa dukan waɗanda suke fama da cututtuka iri-iri, da waɗanda suke da zafin ciwo, da masu aljanu, da waɗanda suke masu farfaɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su.
25. Taron mutane mai yawa daga Galili, Dekafolis, Urushalima, Yahudiya da kuma yankin hayin Urdun suka bi shi.