A A A A A

Mattiyu 20:17-34
17. To, da Yesu yana haurawa zuwa Urushalima, sai ya ja almajiran nan goma sha biyu gefe, ya ce musu,
18. “Za mu haura zuwa Urushalima, za a kuma bashe Ɗan Mutum ga manyan firistoci da malaman dokoki. Za su yi masa hukuncin kisa
19. za su kuma bashe shi ga Alʼummai su yi masa baʼa, su yi masa bulala, su kuma gicciye shi. A rana ta uku kuma a tashe shi!”
20. Sai mahaifiyar ʼyaʼyan Zebedin nan ta zo wurin Yesu tare da ʼyaʼyanta, da ta durƙusa a ƙasa, sai ta roƙe shi yǎ yi mata wani abu.
21. Ya yi tambaya ya ce, “Mene ne kike so?” Ta ce, “Ka sa daga cikin ʼyaʼyan nan nawa biyu, ɗaya yǎ zauna a damarka, ɗaya kuma a hagunka, a mulkinka.”
22. Yesu ya ce musu, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Za ku iya sha daga kwaf da zan sha?” Suka amsa, “Za mu iya.”
23. Yesu ya ce musu, “Hakika za ku sha daga kwaf na, sai dai zama a damana, ko haguna, ba ni nake da izinin bayarwa ba. Waɗannan wurare na waɗanda Ubana ya shirya wa ne.”
24. Da goman suka ji haka, sai suka yi fushi da ʼyanʼuwan nan biyu.
25. Yesu ya kira su wuri ɗaya ya ce, “Kun san cewa masu mulkin Alʼummai sukan nuna musu iko, hakimansu kuma sukan gasa musu iko.
26. Ba haka zai kasance da ku ba. Maimakon haka, duk mai son zama babba a cikinku, dole yǎ zama bawanku,
27. kuma duk mai son zama shugaba, dole yǎ zama bawanku,
28. kamar yadda Ɗan Mutum bai zo don a bauta masa ba, sai dai don yǎ yi bauta, yǎ kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”
29. Saʼad da Yesu da almajiransa suke barin Yeriko, sai wani babban taro ya bi shi.
30. Makafi biyu kuwa suna zaune a bakin hanya, da suka ji cewa Yesu yana wucewa, sai suka ɗaga murya suka ce, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!”
31. Mutane suka tsauta musu, suka ce musu su yi shiru. Sai suka ƙara ɗaga murya suna cewa, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!”
32. Yesu ya tsaya ya kira su. Ya tambaye su, “Me kuke so in yi muku?”
33. Suka amsa suka ce, “Ubangiji, muna so mu sami ganin gari.”
34. Sai Yesu ya ji tausayinsu, ya taɓa idanunsu. Nan da nan kuwa suka sami ganin gari, suka kuma bi shi.