A A A A A

Mattiyu 20:1-16
1. “Mulkin sama yana kama da wani mai gona, wanda ya fita da sassafe don yǎ yi hayar mutane su yi aiki a gonar inabinsa.
2. Ya yarda yǎ biya su dinari guda a yini, sai ya tura su gonar inabinsa.
3. “Wajen saʼa ta uku, ya fita sai ya ga waɗansu suna tsattsaye a bakin kasuwa ba sa kome.
4. Ya ce musu, ‘Ku ma ku tafi gonar inabina ku yi aiki, zan kuwa biya ku abin da ya dace.’
5. Saboda haka suka tafi. “Ya sāke fita a saʼa ta shida da kuma saʼa ta tara, ya sāke yin haka.
6. Wajen saʼa ta goma sha ɗaya, ya sāke fita, ya tarar da waɗansu har yanzu suna tsattsaye. Ya tambaye su, ‘Don me kuke yini tsattsaye a nan ba kwa kome?’
7. “Suka amsa, ‘Don ba wanda ya ɗauke mu aiki.’ “Ya ce musu, ‘Ku ma ku je ku yi aiki a gonar inabina.’
8. “Saʼad da yamma ta yi, sai mai gonar inabin ya ce wa wakilinsa, ‘Kira maʼaikatan, ka biya su hakkin aikinsu, fara da waɗanda aka ɗauke su a ƙarshe har zuwa na farko.’
9. “Maʼaikatan da ka ɗauka wajen saʼa ta goma sha ɗaya suka zo, kowannensu kuwa ya karɓi dinari guda.
10. Saboda haka da waɗanda aka ɗauka da fari suka zo, sun zaci za su sami fiye da haka. Amma kowannensu ma ya karɓi dinari guda.
11. Saʼad da suka karɓa, sai suka fara yin gunaguni a kan mai gonar.
12. Suna cewa, ‘Waɗannan mutanen da aka ɗauka a ƙarshe sun yi aikin saʼa ɗaya ne kawai, ka kuma mai da su daidai da mu da muka yini muna faman aiki, muka kuma sha zafin rana.’
13. “Amma ya amsa wa ɗayansu ya ce, ‘Aboki, ban cuce ka ba. Ba ka yarda ka yi aiki a kan dinari guda ba?
14. Ka karɓi hakkinka ka tafi. Ni na ga damar ba waɗannan na ƙarshe daidai da yadda na ba ka.
15. Ba ni da ikon yin abin da na ga dama da kuɗina ne? Ko kana kishi saboda ni mai kyauta ne?’
16. “Saboda haka fa, na ƙarshe za su zama na farko, na farko kuma su zama na ƙarshe.”