A A A A A

Mattiyu 3:1-17
1. A waɗancan kwanaki, Yohanna Mai Baftisma ya zo, yana waʼazi a Hamadan Yahudiya
2. yana cewa, “Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.”
3. Wannan shi ne wanda aka yi magana ta wurin annabi Ishaya: “Murya mai kira a hamada, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, ku miƙe hanyoyi dominsa.’ ”
4. Tufafin Yohanna kuwa an yi su da gashin raƙumi ne, yana kuma ɗaure da ɗamara ta fata. Abincinsa kuwa fari ne da zumar jeji.
5. Mutane suka zo wurinsa daga Urushalima da dukan Yahudiya da kuma dukan yankin Urdun.
6. Suna furta zunubansu, ya kuma yi musu baftisma a Kogin Urdun.
7. Amma da ya ga Farisiyawa da Sadukiyawa da yawa suna zuwa inda yake yin baftisma, sai ya ce musu: “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku ku guje wa fushin nan mai zuwa?
8. Ku yi ayyukan da suka dace da tuba.
9. Kada ma ku yi tunani za ku iya ce wa kanku, ‘Ai, muna da mahaifinmu Ibrahim.’ Ina gaya muku cewa daga cikin duwatsun nan Allah zai iya ta da ʼyaʼya wa Ibrahim.
10. An riga an sa bakin gatari a gindin itatuwa, kuma duk itacen da bai ba da ʼyaʼya masu kyau ba, za a sare shi a jefa cikin wuta.
11. “Ina muku baftisma da ruwa domin tuba. Amma wani yana zuwa a bayana wanda ya fi ni iko, wanda ko takalmansa ma ban isa in ɗauka ba. Zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da kuma wuta.
12. Matankaɗinsa yana a hannunsa, zai kuma share wurin sussukarsa, yana tattara alkamarsa a cikin rumbu yana kuma ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.”
13. Sai Yesu ya zo daga Galili ya je Urdun don Yohanna yǎ yi masa baftisma.
14. Amma Yohanna ya so yǎ hana shi, yana cewa, “Ina bukata ka yi mini baftisma, yaya kake zuwa wurina?”
15. Yesu ya amsa, ya ce, “Bari yǎ zama haka yanzu; ya dace mana mu yi haka don mu cika dukan adalci.” Saʼan nan Yohanna ya yarda.
16. Nan da nan da aka yi wa Yesu baftisma, sai ya fito daga ruwa. A wannan lokaci sama ya buɗe, sai ya ga Ruhun Allah yana saukowa kamar kurciya ya kuwa sauka a kansa.
17. Sai murya daga sama ta ce, “Wannan shi ne Ɗana wanda nake ƙauna; wanda kuma nake jin daɗinsa ƙwarai.”