English
A A A A A

Mattiyu 18:21-35
21. Sai Bitrus ya zo wurin Yesu ya yi masa tambaya ya ce, “Ubangiji, sau nawa zan yafe wa ɗanʼuwana saʼad da ya yi mini zunubi? Har sau bakwai?”
22. Yesu amsa ya ce, “Ina gaya maka, ba sau bakwai ba, amma sau sabaʼin da bakwai.
23. “Saboda haka, mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya so yǎ yi ƙididdigar dukiyarsa da take a hannun bayinsa.
24. Da ya fara ƙididdigar, sai aka kawo masa wani wanda yake bin bashin talentii dubu goma.
25. Da yake bai iya biya ba, sai maigida ya umarta a sayar da shi da matarsa da yaransa da kuma duk abin da yake da shi, a biya bashin.
26. “Bawan ya durƙusa a gabansa. Ya roƙa, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka ƙaf.’
27. Maigidan bawan ya ji tausayinsa, ya yafe masa bashin, ya kuma sake shi.
28. “Amma da wannan bawa ya fita, sai ya gamu da wani abokin bautarsa wanda yake binsa bashin dinari ɗari. Sai ya cafke shi, ya shaƙe shi a wuya yana cewa, ‘Biya ni abin da nake binka!’
29. “Wannan abokin bautarsa ya durƙusa ya roƙe shi, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka.’
30. “Amma ya ƙi. A maimako, sai ya je ya sa aka jefa shi a kurkuku, sai ya biya bashin.
31. Saʼad da sauran bayin suka ga abin da ya faru, abin ya ɓata musu rai ƙwarai, suka tafi suka faɗa wa maigidansu dukan abin da ya faru.
32. “Sai maigidan ya kira wannan bawa ciki. Ya ce, ‘Kai mugun bawa, na yafe duk bashin da nake binka domin ka roƙe ni.
33. Ashe, bai kamata kai ma ka ji tausayin abokin bautarka yadda na yi maka ba?’
34. Cikin fushi, maigidan ya miƙa shi ga maʼaikatan kurkuku su gwada masa azaba, sai ya biya dukan bashin da ake binsa.
35. “Haka Ubana da yake cikin sama zai yi da kowannenku, in ba ku yafe wa ʼyanʼuwanku daga zuciyarku ba.”