A A A A A

Mattiyu 18:1-20
1. A lokacin nan sai almajirai suka zo wurin Yesu suka yi tambaya suka ce, “Wane ne mafi girma a mulkin sama?”
2. Sai ya kira ƙaramin yaro ya sa shi ya tsaya a tsakiyarsu.
3. Sai ya ce: “Gaskiya nake gaya muku, in ba kun canja kuka zama kamar ƙananan yara, labudda, ba za ku shiga mulkin sama ba.
4. Saboda haka, duk wanda ya ƙasƙantar da kansa kamar wannan yaro, shi ne mafi girma a mulkin sama.
5. “Duk kuma wanda ya karɓi ƙaramin yaro kamar wannan a cikin sunana ya karɓe ni ne.
6. Amma duk wanda ya sa ɗaya daga cikin ƙananan nan da suka gaskata da ni ya yi zunubi, zai fiye masa a rataya babban dutsen niƙa a wuyarsa, a kuma nutsar da shi a zurfin teku.
7. “Kaiton duniya saboda abubuwan da suke sa mutane su yi zunubi! Dole irin waɗannan abubuwa su zo, sai dai kaiton mutumin da ya zama sanadin kawo su!
8. In hannunka ko ƙafarka yana sa ka zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da hannu ko ƙafa ɗaya da hannuwa biyu ko ƙafafu biyu da a jefar da kai cikin madawwamiyar wuta da hannuwa biyu ko ƙafafu biyu.
9. In kuma idonka yana sa ka zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da ido ɗaya, da ka shiga jahannama ta wuta da idanunka biyu.
10. “Ku lura, kada ku rena ɗaya daga cikin waɗannan ƙanana. Gama ina faɗa muku malaʼikunsu a sama kullum suna duban fuskar Ubana da yake cikin sama.
11. ***
12. “Me kuka gani? In wani yana da tumaki ɗari, sai ɗaya daga cikinsu ta ɓace, ba sai yǎ bar tasaʼin da taran a kan tuddai yǎ je neman guda ɗayan da ta ɓace ba?
13. In kuwa ya same ta, ina gaya muku gaskiya, zai yi murna saboda ɗayan fiye da tasaʼin da taran da ba su ɓace ba.
14. Haka ma Ubanku da yake cikin sama ba ya so ko ɗaya daga cikin ƙananan nan yǎ ɓace.
15. “In ɗanʼuwanka ya yi maka laifi, ka je ka nuna masa laifinsa, tsakaninku biyu kaɗai. In ya saurare ka, ka maido da ɗanʼuwanka ke nan.
16. Amma in bai saurare ka ba, ka je tare da mutum ɗaya ko biyu, domin ‘a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku.’
17. In kuwa ya ƙi yǎ saurare su, sai ka gaya wa ikkilisiya; in kuma ya ƙi yǎ saurari ikkilisiya ma, ka yi da shi kamar marar sanin Allah ko mai karɓar haraji.
18. “Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka ɗaure a duniya, za a ɗaure a sama, duk kuma abin da kuka kunce a duniya, za a kunce shi a sama.
19. “Har wa yau, ina gaya muku cewa in mutum biyu a cikinku a duniya suka yarda su roƙi wani abu, Ubana da yake cikin sama zai yi muku.
20. Gama inda mutum biyu ko uku suka taru cikin sunana, a can ma ina tare da su.”