A A A A A

Mattiyu 17:1-26
1. Bayan kwana shida, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, Yaƙub da Yohanna ɗanʼuwan Yaƙub, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, su kaɗai.
2. A can aka sāke kamanninsa a gabansu. Fuskarsa ta haskaka kamar rana, tufafinsa kuwa suka zama fari fat suna walƙiya.
3. Nan take sai ga Musa da Eliya suka bayyana a gabansu, suna magana da Yesu.
4. Sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ya yi kyau da muke nan. In kana so, sai in kafa bukkoki uku--ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Eliya.”
5. Yayinda yake cikin magana, sai wani girgije mai haske ya rufe su, sai wata murya daga cikin girgijen ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna; wanda kuma nake jin daɗinsa ƙwarai. Ku saurare shi!”
6. Saʼad da almajiran suka ji haka, sai suka fāɗi ƙasa rubda ciki, a firgice.
7. Amma Yesu ya zo ya taɓa su ya ce, “Ku tashi, kada ku ji tsoro.”
8. Da suka ɗaga kai, ba su ga kowa ba sai Yesu kaɗai.
9. Suna cikin gangarowa daga dutsen ke nan, sai Yesu ya umarce su cewa, “Kada ku faɗa wa kowa abin da kuka gani, sai bayan an ta da Ɗan Mutum daga matattu.”
10. Almajiran suka tambaye shi suka ce, “To, me ya sa malaman dokoki suke cewa, dole sai Eliya ya fara zuwa?”
11. Yesu ya amsa, ya ce, “Tabbatacce, Eliya zai zo, zai kuma gyara dukan abubuwa.
12. Amma ina faɗa muku, Eliya ya riga ya zo, ba su kuwa gane shi ba, amma suka yi masa duk abin da suka ga dama. Haka ma Ɗan Mutum zai sha wahala a hannunsu.”
13. Saʼan nan almajiran suka gane cewa yana musu zancen Yohanna Mai Baftisma ne.
14. Da suka isa wajen taron, sai wani mutum ya zo ya durƙusa a gabansa.
15. Ya ce, “Ubangiji, ka yi wa ɗana jinƙai. Yana da farfaɗiya yana kuma shan wahala ƙwarai. Ya sha fāɗuwa cikin wuta ko ruwa.
16. Na kuma kawo shi wurin almajiranka, amma ba su iya warkar da shi ba.”
17. Yesu ya amsa, ya ce, “Ya ku zamani marasa bangaskiya da kuma masu taurin kai, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe kuma zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron a nan.”
18. Yesu ya tsauta wa aljanin, ya kuwa rabu da yaron, nan take yaron ya warke.
19. Saʼan nan almajiran suka zo wurin Yesu a ɓoye suka tambaye shi suka ce, “Me ya sa ba mu iya fitar da aljanin ba?”
20. Ya amsa ya ce, “Saboda kuna da ƙarancin bangaskiya sosai. Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiyar da take ƙanƙanuwa kamar ƙwayar mustad, za ku iya ce wa wannan dutse, ‘Matsa daga nan zuwa can,’ zai kuwa matsa. Babu abin da zai gagare ku.”
21. ***
22. Da suka taru a Galili, sai ya ce musu, “Za a bashe Ɗan Mutum, a hannun mutane.
23. Za su kashe shi, a rana ta uku kuma za a tashe shi.” Almajiran kuwa suka cika da baƙin ciki.
24. Bayan Yesu da almajiransa suka isa Kafarnahum, sai masu karɓan harajin rabin shekel suka zo wurin Bitrus suka ce, “Malaminku ba ya biyan harajin haikali ne?”
25. Ya amsa ya ce “I, yana biya.” Da Bitrus ya shiga gida, Yesu ne ya fara magana. Ya ce masa, “Me ka gani, Siman? Daga wurin wane ne sarakunan duniya suke karɓar kuɗin shiga da kuma haraji-daga wurin ʼyaʼyansu ne ko kuwa daga wurin waɗansu?”
26. Bitrus ya amsa, ya ce, “Daga wurin waɗansu.” Yesu ya ce masa, “Wato, an ɗauke wa ʼyaʼyan ke nan.”