English
A A A A A

Mattiyu 16:1-28
1. Farisiyawa da Sadukiyawa suka zo don su gwada Yesu ta wurin neman yǎ nuna musu wata alama daga sama.
2. Ya amsa ya ce, “Saʼad da yamma ta yi, kukan ce, ‘Yanayi zai yi kyau, gama sararin sama ya yi ja,’
3. da safe kuma, ku ce, ‘Yau kam za a yi hadari, gama sararin sama ya yi ja, ya kuma ɓata fuska.’ Kun san yadda za ku fassara yanayin sararin sama, amma ba kwa iya fassarar alamun lokatai.
4. Wannan mugu da mazinacin zamani yana neman wani abin banmamaki, amma ba wata alamar da za a nuna wa wannan zamani sai dai ta Yunana.” Sai Yesu ya bar su ya tafi abinsa.
5. Da suka ƙetare tafkin, almajiran sun manta su riƙe burodi.
6. Yesu ya ce musu, “Ku yi hankali, ku yi taka tsantsan da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa.”
7. Sai suka fara tattaunawa da junansu suna cewa, “Ko don ba mu kawo burodi ba ne.”
8. Sane da abin da suke zance, sai Yesu ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, don me kuke magana da junanku a kan ba ku zo da burodi ba?
9. Har yanzu ba ku gane ba ne? Ba ku tuna da gurasa biyar ɗin nan na mutum dubu biyar ba? Kwando nawa kuka tattara cike?
10. Ko kuma burodi bakwai nan na mutum dubu huɗu, cikakku manyan kwanduna nawa kuka ɗauka?
11. Yaya kuka kāsa gane cewa ba zancen burodi nake yi ba? Sai dai ku yi hankali da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa.”
12. Saʼan nan suka gane ba cewa yake musu su yi hankali da yistin da ake amfani da shi a burodi ba ne, sai dai su yi hankali da koyarwar Farisiyawa da Sadukiyawa ne.
13. Saʼad da Yesu ya zo yankin Kaisariya Filibbi, sai ya tambayi almajiransa ya ce, “Wa mutane suke ce da Ɗan Mutum?”
14. Suka amsa, “Waɗansu suna ce Yohanna Mai Baftisma; waɗansu kuma suna ce annabi Eliya; har wa yau waɗansu suna ce Irmiya ne ko kuma ɗaya daga cikin annabawa.”
15. Ya tambaye su, “Amma ku fa, wane ne ni a ganinku?”
16. Siman Bitrus ya amsa, ya ce, “Kai ne Kiristi, Ɗan Allah mai rai.”
17. Yesu ya amsa, ya ce, “Mai albarka ne kai Siman ɗan Yunana, gama ba mutum ne ya bayyana maka wannan ba, sai dai Ubana da yake cikin sama.
18. Ina kuwa gaya maka, kai ne Bitrus, a kan wannan dutse zan gina ikkilisiyata, kuma ƙofofin Hades ba za su rinjaye ta ba.
19. Zan ba ka mabuɗan mulkin sama; kome ka ɗaure a duniya zai zama a ɗaure a sama, kome kuma ka kunce a duniya zai zama a kunce a sama.”
20. Saʼan nan ya gargaɗi almajiransa cewa kada su faɗa wa kowa shi ne Kiristi.
21. Tun daga wannan lokaci Yesu ya fara bayyana wa almajiransa cewa dole yǎ tafi Urushalima yǎ sha wahaloli da yawa a hannun dattawa, manyan firistoci da kuma malaman dokoki, dole a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.
22. Bitrus ya ja shi gefe ya fara tsauta masa yana cewa, “Sam, Ubangiji! Wannan ba zai taɓa faruwa da kai ba!”
23. Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Rabu da ni, Shaiɗan! Kai abin sa tuntuɓe ne a gare ni; ba ka tunanin alʼamuran Allah, sai dai alʼamuran mutane.”
24. Saʼan nan Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk mai son bin na, dole yǎ ƙi kansa, yǎ ɗauki gicciyensa, yǎ bi ni.
25. Gama duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, zai same shi.
26. Me mutum zai amfana in ya sami duniya duka, amma ya rasa ransa? Ko kuwa me mutum zai bayar a bakin ransa?
27. Gama Ɗan Mutum zai zo cikin ɗaukakar Ubansa, tare da malaʼikunsa, saʼan nan zai ba wa kowane mutum lada gwargwadon abin da ya yi.
28. Gaskiya nake gaya muku, waɗansu da suke tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba sai sun ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin mulkinsa.”