A A A A A

Mattiyu 15:21-39
21. Barin wurin ke nan, sai Yesu ya janye zuwa yankin Taya da Sidon.
22. Wata Bakanʼaniya daga wajajen ta zo wurinsa, tana ihu tana cewa, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai! ʼYata tana shan wahala ƙwarai daga aljanin da yake cikinta.”
23. Yesu bai ce mata uffan ba. Saboda haka almajiransa suka zo wurinsa suka roƙe shi suka ce, “Ka kore ta ta tafi, tana ta binmu tana damunmu da ihu.”
24. Ya amsa ya ce, “An aiko ni wurin ɓatattun tumakin Israʼila ne kaɗai.”
25. Sai macen ta zo ta durƙusa a gabansa ta ce, “Ubangiji, ka taimake ni!”
26. Ya amsa ya ce, “Ba daidai ba ne a ɗauki abincin yara a jefa wa karnukansu.”
27. Ta amsa ta ce, “I, Ubangiji, amma karnuka ma sukan ci gutsattsarin da sukan fāɗi daga teburin maigidansu.”
28. Saʼan nan Yesu ya amsa, ya ce, “Mace, kina da bangaskiya mai yawa! An biya miki bukatarki.” ʼYarta kuwa ta warke nan take.
29. Yesu ya tashi daga nan ya bi ta gefen Tekun Galili. Saʼan nan ya haura gefen wani dutse ya zauna.
30. Taron mutane mai girma kuwa suka zo wurinsa, suna kawo masa guragu, makafi, shanyayyu, kurame da dai waɗansu da yawa, suka kuwa kwantar da su a gabansa; ya kuma warkar da su.
31. Mutanen kuwa suka yi mamaki saʼad da suka ga kurame suna magana, shanyayyu suna samun lafiya, guragu suna takawa, makafi kuma suna ganin gari. Sai suka yabi Allah na Israʼila.
32. Yesu ya kira almajiransa wurinsa ya ce, “Ina jin tausayin mutanen nan; gama kwana uku ke nan suke tare da ni ba abin da za su ci. Ba na so in sallame su da yunwa, don kada su kāsa a hanya.”
33. Sai almajiransa suka amsa suka ce, “Ina za mu sami isashen burodi a wannan wurin da babu kowa mu ciyar da irin taron nan?”
34. Yesu ya tambaye su, “Burodi guda nawa kuke da shi?” Suka amsa suka ce, “Guda bakwai da ʼyan ƙananan kifaye.”
35. Ya sa taron su zazzauna a ƙasa.
36. Saʼan nan ya ɗauki burodi guda bakwai da kuma kifayen nan, da ya yi godiya, sai ya kakkarya su ya ba wa almajiran, su kuma suka ba wa mutane.
37. Duk kuwa suka ci, suka ƙoshi. Daga baya almajiran suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna bakwai.
38. Yawan waɗanda suka ci kuwa, maza dubu huɗu ne, ban da mata da yara.
39. Bayan Yesu ya sallami taron, sai ya shiga jirgin ruwa ya tafi wajajen Magadan.