English
A A A A A

Mattiyu 15:1-20
1. Saʼan nan waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki suka zo wurin Yesu daga Urushalima suka yi tambaya suka ce,
2. “Me ya sa almajiranka suke karya alʼadun dattawa? Ba sa wanke hannuwansu kafin su ci abinci!”
3. Yesu ya amsa, ya ce, “Ku ma me ya sa kuke karya dokar Allah saboda alʼadarku?
4. Gama Allah ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, kuma duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa dole a kashe shi.’
5. Amma ku kukan ce, in wani ya ce wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa, ‘Duk taimakon da dā ya kamata za ku samu daga gare ni an ba wa Allah,’
6. ba zai ‘girmama mahaifinsa’ da shi ba. Ta haka kun yi banza da maganar Allah saboda alʼadarku.
7. Ku munafukai! Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku da ya ce:
8. “ ‘Waɗannan mutane da baki kawai suke girmama ni, amma zukatansu suna nesa da ni.
9. A banza suke mini sujada, koyarwarsu, dokoki ne kawai da mutane suke koyarwa.’ ”
10. Sai Yesu ya kira taron wurinsa ya ce, “Ku saurara ku kuma gane.
11. Abin da yake shiga bakin mutum ba ya ‘ƙazantar’ da shi, sai dai abin da yake fitowa daga bakinsa, shi ne yake ‘ƙazantar’ da shi.”
12. Sai almajiran suka zo wurinsa suka ce, “Ka san cewa Farisiyawa ba su ji daɗi saʼad da suka ji wannan ba?”
13. Ya amsa ya ce, “Duk tsiron da Ubana na sama bai shuka ba, za a tumɓuke shi daga saiwoyi.
14. Ku ƙyale su, ai, makafin jagorai ne. In makaho ya yi wa makaho jagora, dukansu za su fāɗa a rami.”
15. Bitrus ya ce, “Ka bayyana mana wannan misali.”
16. Yesu ya tambaye, su ya ce, “Har yanzu ba ku gane ba ne?
17. Ba ku gane cewa duk abin da ya shiga baki yakan wuce ciki ne daga nan kuma yǎ fita daga jiki ba?
18. Amma abubuwan da suke fitowa ta baki suna fitowa ne daga zuciya, su ne kuma suke ‘ƙazantar’ da mutum.
19. Gama daga zuciya ne mugayen tunani, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar ƙarya, ɓatan suna, suka fitowa.
20. Waɗannan su ne suke ‘ƙazantar’ da mutum; amma cin abinci ba tare da wanke hannuwa ba, ba ya ‘ƙazantar’ da mutum.”