A A A A A

Mattiyu 14:22-35
22. Nan da nan Yesu ya sa almajiran su shiga jirgin ruwa su sha gabansa, su haye zuwa ɗayan hayin, yayinda shi kuma yǎ sallami taron.
23. Bayan ya sallame su, sai ya haura bisan gefen dutse shi kaɗai don yǎ yi adduʼa. Da yamma ta yi, yana can shi kaɗai,
24. jirgin ruwan kuwa ya riga ya yi nesa da gaci, yana fama da raƙuman ruwa domin iska tana gāba da shi.
25. Wajen tsaro na huɗu na dare, sai Yesu ya nufe su, yana takawa a kan tafkin.
26. Saʼad da almajiran suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai tsoro ya kama su. Suka yi ihu don tsoro suka ce, “Fatalwa ce.”
27. Amma nan da nan Yesu ya ce musu, “Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro.”
28. Sai Bitrus ya amsa, ya ce, “Ubangiji in kai ne ka ce mini in zo wurinka a kan ruwan.”
29. Ya ce, “Zo.” Sai Bitrus ya fita daga jirgin ruwan, ya taka a kan ruwan ya nufe wajen Yesu.
30. Amma da ya ga haukar iskar, sai ya ji tsoro, ya kuma fara nutsewa, sai ya yi ihu ya ce, “Ubangiji, ka cece ni!”
31. Nan da nan Yesu ya miƙa hannu ya kamo shi ya ce, “Kai mai ƙarancin bangaskiya, don me ka yi shakka?”
32. Da suka hau jirgin ruwan, sai iskar ta kwanta.
33. Waɗanda suke cikin jirgin ruwan kuwa suka yi masa sujada, suna cewa, “Gaskiya kai Ɗan Allah ne.”
34. Saʼad da suka haye, sai suka sauka a Gennesaret.
35. Da mutanen wurin suka gane da Yesu, sai suka kai labari a koʼina a ƙauyukan da suke kewaye. Mutane suka kawo masa dukan marasa lafiyarsu